Recent Updates

FACALA Page 9

  9

Khamis ta saka a gaba da magiya tunda ya yarda zai kaima ZamZam kayanta da tace masa ta manta

"Muje tare dan Allaah, kaji Dee? In dan sha iska, tunda akayi auren nan fa babu inda naje"

Ya kama bakinshi yana kallonta cike da mamaki

"Yanzun kwana nawa ne da auren da kike cewa babu inda kikaje? So kike Mummy tayi mun fada idan taji mun fita tare ko?"

Itace take kallonshi da mamaki yanzun

"Fada? Saboda mun fita?"

Ta kasa hakuri ta tambaya, sai ya danyi wani karamin murmushi

"Zatace nine na jaki yawo ko gajiyar biki baki gama warwarewa ba"

Zancen bai zaunawa Raihana ba, amman da yake so takeyi ta fitan sai ta basar

"Yanzun fa zamuje mu dawo, ko shiga gidan ba zanyi ba, kiranta zanyi ta fito ta karba, nima ai idan akaji na fito za'ayi mun fada a gidanmu... kaji, dan Allaah"

Ita fa wannan dalilin na daya daga cikin abubuwan da suka kara haska mata Khamis, motar da yake da ita, balle ma daga haduwarsu, kafin auren ya kara sake wata motar, tana zaune sai ta dinga hango yanda zasu dinga fita tare dashi suna zagaye gari, irin dan abu kadan din nan zaice ta shirya ta rakashi, wata rana ma outing zasu fita, yana tuki yana dan miko hannunshi daya yana rike nata. Daya daga mata kai alamar ta shirya, sai da t a buga tsalle ta rungume shi tana sumbatar fuskarshi, dariya yayi kawai

"Ki shirya to, bana so muyi yamma sosai, kinga da anyi magriba zan dawo in tafi asibiti..."

Wannan ne karo na farko da zai fara night shift tunda sukayi aure, yabi duk ya damu, tunda safe yake ce mata ko ya kira mata su Ikhlas su tayata kwana, tace masa

"Haba kamar dai wani abu, bafa ni kadai bace a gidan, normal ne karka wani damu"

Ya dan bata fuska

"Normal ne ko? Zaki kwana ke kadai, batare dani ba kina kiran normal ne? Irin zaki walala babu takurata ko?"

Sai ta kashe masa ido daya, ya mika hannu zai rikota ta goce tana masa dariya. Kuma kamar yanda tace masa din, normal ne, ita bata da matsala da kwana ita kadai a gida, komin girmanshi, balle kuma irin wannan gidan da kasan akwai mutane zagaye da kai ko ta ina, tsoron me zataji? Brown din yadi mai duhu ya saka a jikinshi da ya haska farar fatarshi, sai ya saka hularshi milk color, haka takalmanshi ma. Da Raihana taga hular daya dauko, sai ta zabo wata abayarta ta cikin lefe kalar hular tashi, irin abayas din nan ne masu fadi, dan haka ma sai tayi rolling din mayafin abayar bayan ta saka hula, jambaki kawai ta dan goga ma labbanta, tayi kyau, sai kamshi suke bazawa na turarukan da suka fesa daga ita har Khamis din, haka kawai ta dauki bakar jaka ta takalmin da ta saka.

Ba saita jira wanu ya gaya mata ba, sunyi kyau. Murmushinta ya kasa boyuwa da Khamis ya riko mata hannu

"Ke dai Allaah Yasa mu auri mijin da ba zamuji kunyar nunawa 'yan uwa da abokan arziki ba"

Haka ZamZam ta taba ce mata da takeyi mata gulmar wata 'yar islamiyyarsu da akace ta auri wani Alhaji

"Irin tiliqeqen nan ne, su Habiba sunce katon cikine dashi, makirar shisa taki gayyatar kowa dinner dan kar a ganshi ayi mata dariya"

Raihana ta karashe maganar da dariya, sai dai ita ZamZam abin bai bata dariya ba sam, dan bayan tayi wannan addu'ar saida ta dora da

"Ni kam in da gaske boyeshi takeyi dan kar ayi mata dariya, ta bani mamaki, kuma banji masa dadi ba, ina amfanin ka auri macen da take kunyar nuna ka?"

Tabe baki Raihana tayi

"Ke yanzun kika auri wannan sai ki nuna ma kawayenki?"

ZamZam tayi murmushi

"Su waye ma kawayen nawa? Bake bace ba? Kuma akan me zanji kunya? Ni da na zabeshi muyi zaman aure, ai zancen kunya ta kare, wallahi nuna kayana zanyi, wanda yayi dariya sai ya saka tsani ya hau ya gayawa wanda ya halicce shi abinda baiyi ba a jikinshi"

Sai Raihana ta daga hannayenta sama

"Karki hadani da Allaah...nayi shiru"

Kuma tun randa ta fito daga gidansu ta hangi Khamis tsaye, ya jingina jikin motar shi ya harde hannayenshi a kirji, suna hada ido yayi mata murmushin nan, daga inda take tana hango yanda kumatunshi ya lotsa. A wannan ranar taji tayi miji 

Mijin da zata dauki kayanta akai, ta zagaya ta nuna shi cike da alfahari!
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Haka suka taka suka fita abinsu, gidanma kofar kawai suka janyo, ko mukulli bata ga Khamis ya saka ba

"Ba zaka rufe kofar ba"

Saiya girgiza mata kai

"Babu wanda zai shiga ai..."

Ta dauka ma Khamis zai karbi ledojin data dauko saboda sunyi mata nauyi, yatsunta har sun sage, sai bata ga yayi hakan ba, mota ma ita ta bude bangaren da zata zauna, dan juyawa ma yayi da sauri ya koma cikin gidan yana gaya mata ya manta wayarshi. Anan gabanta ta saka ledojin ta zauna tana jiranshi.

"Hamma fita zakuyi?"

Raihana taji an tambaya, data duba sai taga Alina ce, dan sun hada ido, amman yarinyar batayi tunanin gaishe da ita ba

"Ba nisa zamuyi ba Alina, sako kawai zamu mika ma kawar Antynki"

Ta dan kada idanuwanta, dan Raihana taga lokacin da ta dan tabe baki ma, harshe ta sauya tayi masa magana, sun danyi musayar maganar kusan sau nawa, kafin Khamis din ya sauke numfashi yana furta

"Karki bata mana lokaci Alina, kiyi sauri ki fito"

Da gudu Raihana taga ta juya

"Kace fa baka so muyi yamma"

Raihana ta fada ranta a dan bace, dan so take ta tabbatar da abinda ta fahimci ya faru

"Yanzun zamu tafi, Alina naso ta dan sha iska, wai zata rakamu, yanzun zata fito..."

Kallon Khamis takeyi, amman sai taga wayarshi yake dannawa daga tsayuwar da yayi kamar babu wani abu na daban akan abinda ya fada, da Alina ta tashi ba ita kadai ta fito ba, su hudu Raihana ta gani. Kafin kuma ta gama mamaki ta hango Adda Badr a bayansu, su Ikhlas Abayoyine a jikinsu, ita kuma Addan ta saka wata riga ce bubu, ta leshi sai tayi rolling din mayafinta, a yanda take ba zakace ta haifi Ikhlas da Jawda ba

"Adda wai harda ke aka fito?"

Khamis ya tambayeta, duk da Raihana bataji ko digon mamaki a muryarshi ba, kamar dai abune da ba bako ba, abune da suka saba

"Garin ne naji da zafi, gara mu sha iskar gabaki daya, saika biyo damu mu dan siyi ko ice cream ne da wasu abubuwan"

Yayi dariya

"Aljihunki zamu shiga kenan"

Itama dariyar tayi tana sauya masa harshe 

"Allaah Adda ke zaki dauki nauyinmu"

Daya bude motar ya zauna, su suka bude bayan, sai ji tayi Adda na fadin

"Gaskiya Jawda ki koma gaba ku zauna da Raihana, zamu matse anan..."

Jawdan ta fita tana rufe musu kofar, harta bude gaban, Raihana ta koma kamar mai kallon wata dirama a gidan talabijin

"Dan matso mata nan Ray...Jawda karki matsemun mata ni dai"

Sai ta rike haba

"Baffaa..."

Sai yayi murmushi, Badr da take gidan baya takai hannu tana make masa bayan kai

"A gabana Kham? Lallai baka da kunya"

Duka suka saka dariya, yanda Jawda ta turmutso tana murjema Raihana cinya ya tilasta mata matsawa babu shiri, amman baiyiwa Jawdan ba, dan sosai ta turmutsa tayi bake-bake, Raihana kamar zata hau kan giyar motar

"Saikin dan gyara zamanki fa..."

Cewar Khamis, ta kalle shi tanajin kamar ta shakare shi, ta gyara zamanta taje ina? Sai dai shi bama ita yake kallo ba, asali ma wani abune da Huda ta fada ya bashi dariya. Haka yaja motar suka fice daga gidan, sun kaure motar da hira, sunyi aji daya da yarbawa a sakandiri, su bakwai ne, amman in suka kaure da hira sai kwakwazonsu ya cika ajin har sun janyo ma kowa duka. Ashe suma fulanin haka suke da wannan rakadin, ko kuma su Khamis dinne kamar an saka musu lasifika zasu hau mimbari. Abinda yafi komai kona mata rai, bama wargaza mata wannan fitar da ta gama tsarawa cikin kanta bane kawai, harda yanda basu kulata ba.

Yaran nan babu wanda ya gaisheta, itama bata gaishe da Adda Badr ba, amman ai Addar ce batama kalli inda take ba. Numfashinta har wani hawa da sauka yakeyi saboda bacin rai, ko kadan bata kula da sun shiga unguwarsu ba saida Khamis yayi mata magana

"Dan kirata ta fito da sauri, kinga bana so mu jima a waje..."

Kamar an cusa mata tsumma a baki tace

"Bara na mika mata kawai"

Taya zataso ma ZamZam ta fito ta ganta gwamutse a gaban motar Khamis haka? Ita da taso suyi shigowa irin ta indiyawa, wai wanne ma irin abune wannan? Idan su Alina basu da lissafi, har Adda Badr din ma lissafin ya kwace mata ne? Haka ta tattara ledojin data ajiye, tana raba Jawda data ke yatsina fuska tana fadin
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: "Kai wacce irin unguwa ce wannan? Kinji wani irin zarni ko ta ina yake fitowa oho..."

Kafin Raihana ta wuce tana juyo Adda Badr na fadin

"Ki shigo ciki dan ub*nki, saikin shakarwa kanki wata wahalar, ki ja mana kofar kuma, Khamis daga mana gilasan motar please..."

Wani irin abu ya taso yayi ma Raihana rumfa, ta karewa unguwar tasu kallo. Tasan ba unguwar masu kudi bace ba, amman akwai masu rufin asiri sosai akan layin nasu, wasu gidajen ma harda bene sun dora, sannan ana kokari matuka wajen tsaftace unguwar, kudi ake hadawa gida-gida, a gyara kwatocin, a kwashe duk wata bola, ko yanzun dinma unguwar fes take, ita dai bata ga aibunta ba, kuma babu wani zarni tunda ba fitsari akeyi musu ba. Yanda Jawda tayi maganar cikin raini da izgili ba karamin bakanta mata rai yayi ba. Sai da ta tsaya soron gidansu ZamZam ta dan daidaita kanta, ta dora murmushi akan fuskarta sannan ta shiga da sallama

"Raihana..."

Hajiyayye da take tsakar gidan ta fada cikin mamaki, a kunyace Raihana ta gaishe da ita, tana kokarin fadawa dakin ZamZam 

"Oh yaran yanzun, ke Raihana har kin fito? Me ma ya fito dake...ga kawar taki ta shiga bayi kamar"

Wani sanyi ya ratsata, dan haka data tura kofar dakin ZamZam din saita ajiye mata ledojin nan, da dan gudunta tace

"Mantuwa tayine da taje gidana Hajiyayye, shine mukazo kawo mata, yana jirana a waje..."

Kafin ma Hajiyayye ta amsa harta fice kamar wadda taga wani abin tsoro, sauri tayi kamar zata tuntsira ta karasa wajen motar, sai Jawda ta bude ta fito

"Karki damu, ki shiga daga ciki kawai sai in zauna bakin kofar..."

Cewar Raihana, dan ba karamin matseta Jawda tayi ba, koya Khamis yazo canza giya saiya buge mata kashin kugunta, Jawda ta wani tura baki irin na yaran da suke kan tashen balaga

"Lallai, aini bana iya zama a wani waje in ba kusa da window ba..."

Wani kallo Raihana tayi mata

"Ray bata zama sai a window side, ki shigo mu tafi dan Allaah, sauri fa nakeyi..."

Bataso ta bude bakinta, hawayen bakin cikine zasu zubo mata. Haka ta shiga, da Jawda ta shigo wannan karin saida ta take mata yatsun kafa, kuma yanayin yanda ta takata din yasa taji da gangan tayi. Ta janye kafarta, haka suka sake tafiya, ko sunan wajen da Khamis din ya tsaya dasu bata tsaya dubawa ba, da zasu fita ma ca tayi masa

"Kuje ku dawo kawai..."

Haka daya tambayi me za'a taho mata dashi ta sake amsawa da

"Babu komai"

Sun dan dauki lokaci, suka fito da tarin ledoji, suka dora da hirarsu kamar yanda sukayi har suka isa gida. Da suka dauki ledojin nan, sai Khamis yace mata

"Muje bangaren Mummy"

Muryarta a shaqe tace

"Inaso in shiga bayi, kuje kawai"

Sai kuwa suka tafi din, tabi bayan Khamis da kallo, wai ko dai bai kula da ranta a bace yake ba? Anya? Khamis da ko gajiya tayi yana karantar hakan a muryarta idan suna waya, ya dinga lallabata kenan da kar ta tsaya wani abin, ta kwanta ta huta

"Banason jin muryarki a gajiye haka Ray..."

Balle kuma ace ranta ne ya baci, sau nawa ya baro asibiti yazo gidansu

"Zan ganki ne, in tabbatar kina lafiya"

Taya zai kasa fahimtar ranta a bace yake? Haka ta shige bangarensu, anan falo ma ta fige gyale da hularta ta wula su kan kujera, ta samu waje ta zauna, sai ranta ke kara baci, musamman ma da har aka kira sallar magriba bata ga shigowar Khamis ba, dole ta tashi taje tayi alwala ta gabatar da tata sallar, tana zaune akan darduma ya shigo, yayi sallama, ta kuma amsa a cikin zuciyarta, tana ta kallonshi harya rage kayan jikinshi ya watso ruwa ya fito, a gurguje yake shiryawa yana kallon agogon dake makale a jikin bangon dakin, harya karasa

"Ki taso muje, Mummy tace kije ki kwana a bangarenta kar in barki ke kadai"

Ta kalle shi, so take ta gane abinda yake nufi, dan kamar ba hausa yayi mata ba haka taji

"Babe..."

Yaja sunan yana kallonta kamar yanda take kallonshi 

"Na gaya mata zanyi aikin kwana ne, tace gaskiya ba za'a barki ki kwana ke kadai ba"

Gajiya ce taji ta saukar mata kamar tayi aikin surfe, gajiyar da batasan ta inda take tasowa ba

"Na dauka mun gama magana na fada maka bani da matsala da kwana ni kadai...me yasa zanje can?"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: A hankali take ganin yanayin fuskarshi yana canzawa

"Gaskiya zan kwanta anan, ba sai naje wani waje ba"

Fuskar tashi daice take kara canzawa

"Mummy nace miki tace kije can ki kwana"

Bata cire idanuwanta daga cikin nashi ba tace

"Eh naji ai, ka fada mata lafiya kalau zan kwana ni kadai"

Sai taga yayi dariya, irin dariyar nan da bata da alaka da nishadi, kamar kuma dariya ce da take fassara irin rashin hankalin da yake tunanin tayi a maganarta

"Dan Allaah ki tashi Ray, baki san Mummy ba ko?"

Gani tayi fa da gaske yakeyi

"Zaki sa inyi latti, ki tashi dan Allaah, mayafinki kawai zaki dauka, na tabbata akwai komai da zaki bukata"

Taji idanuwanta sun tara kwallar da ta kasa tarbewa sai da ta zubo, ganin hakan yasa shi zuwa da sauri yana tsugunnawa a gabanta, ya riko hannuwanta, kamar hakan take jira, sai kawai ta fashe da kuka, gabaki daya sai ya rude, dan ya rasa dalilin kukan nata

"Menene? Me ya faru?"

To ta ina zata fara yi masa bayani? Me zatace? Duka auren nasu kwana nawa ne yau? Ya kamata ace ta fara wani korafi ne? Sai ta girgiza masa kai, ta kasa tsaida hawayenta, yasa hannu yana share mata su

"Dan Allaah kiyi hakuri idan ma wani abinne, gidan Mummyn ne bakyaso kije ki kwana?"

Kai ta girgiza a hankali

"To menene?"

Ta sake girgiza kan, hawayen yake ta goge mata, ya sumbaci fuskarta dama da haggu da duk inda labbanshi suka samu

"Muje ki wanke fuskarki, so kike in kasa aikina cikin natsuwa umm?"

Shi ya nade hannun rigarshi da yake dogone, ya wanke mata fuskar, yanda yake ta faman lallashinta yayi kasa da wannan muryar tashi, shine abinda ya dan saukaka mata takurewar da zuciyarta tayi. Amman har ta dauki mayafinta, kwanan gidan Mummy yaki zauna mata. Ko kadan bata hangowa kanta fuskantar wata matsala a auren Khamis ba, musamman irin wannan, shisa takejin kanta yayi murfi, ta rasa ta ina zata fara, komai da ta tsara ne take hango rushewarshi, kamar mikakkiyar katangace da kawai bulallukan ne takeji suna rikito mata, tama kasa daga kanta balle ta ga ta inda matsalar take...
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: 10

No comments