Recent Updates

FACALA Page 1


FACALA BY LubnaSufyan

1

20th June, 2014

Kunshin da yake zane akan hannayenta take kallo, duk da dare ne, sannan haske bai wadaci dakin ba, kwayayene guda hudu, a kowanne bango, sai dai kamar biyu daga cikinsu sun lalace gabaki daya, cikin biyun da suka rage kuma dayane kawai yake da haske, dayan hasken ya zuke kamar shima yana gab da daukewa. Ranar Juma'a ce, daren Asabar, wani dare da idan sun riski safiyarshi zata kafa tarihi mai girman gaske a 'yar karamar duniyarsu ita da Raihana.

Ta lumshe idanuwanta, ta kuma budesu akan lallen dai, zanen bakine, sai akabi wasu daga cikin hudojin filawar aka cikesu da jan rani, sunyi kyau. Ba ita kadai ta gani ba, har mutanen da suke gidan ranar da akayi kunshin sai da suka dinga yabawa

"Anya baki karawa mai lallen nan kudi ta bayan fage ba?"

Wata kawarsu ta fada cikin sigar tsokana, wasu kuma sukace

"Kamar dai kece amaryar ZamZam..."

Kamar dai itace
Da yanzun itace...

Wani sashi na zuciyarta da ta dauka ta jima da rufe masa baki ya furta mata, taji sanyi ya kadata, kamar sai lokacin jikinta yake tuna akwai fankar da take aiki a dakin. Yau daya dai, yau kawai, ai bata aikata zunubi ba dan tabar wannan sashin ya jera mata da yanzun___ idan ma ta sake lumshe idanuwanta har ranar da ita da Raihana suka fara haduwa da Khamis zata tuna, shekara daya da wata biyu. Lokacin damuna ne, an kwana aka kusan yini ana lafta ruwa, kuma ko da suka fito da yammar ko ina a jike yake, har bangwayen gidaje idan ka kalla kasan sun sha ruwan nan sun koshi.

"Tsakani da Allaah Ray kina da 'yar matsala...ke in kikaso abu babu wanda zai huta. Wai ub*n me ma zakiyi da kayan yau da dole sai a yau zaki karbesu?"

Cewar ZamZam da kafarta ta fada cikin wani tarin tabo, duk kuwa da safar data saka kafin zira takalmanta, tanajin yanda ruwan tabon ya ratsa safar yana taba fatarta

"Ke kinsan halin Deeni ai, nifa nace masa ankon bikine dan in samu ya dinka mun, banaso ya gane karya na shirga masa, gara muje yau din, harfa dari bakwai na kara masa akan kudin saboda emergency ne"

Karamin tsaki ZamZam taja, taja mayafinta da iska ke barazanar figewa, tana kara gyara masa zama.

"Dole saina samu ruwa na wanke kafata..."

Raihana ta juya ta kalli kafar, sai kawai dariya ta kwace mata, ZamZam ta watsa mata harara

"Wallahi sai in koma gida"

Raihana na dariyar data kasa tsayarwa tace

"Yi hakuri kawata...kema dan Allaah ya za'ayi kisa wannan skirt din, ba dole ki dinga tafiya a harde ba..."

Skirt ne da hango kanta a cikinshi da Raihana tayi kawai yasa taji gwiwoyinta na mata ciwo, dan ya kama ZamZam ya zauna a wannan faskeken kugun nata kamar a jiki aka dinka shi, sannan ya matse ta wajen gwiwar ya kuma bude daga kasa, ba zata tuna pieces nawa teloli suke kiranshi ba, dan ita batason duk wani abu da zai takurata, ko dama in tanaso din gidansu babu mai barinta fitowa da irin shigar da take jikin ZamZam, tasan bata da abinda ma zata tsuke din, ita din irin siraran matan nan ne. Ba kamar ZamZam da kai tsaye ba zaka kirata da mai kiba ba, amman a murje take, ko ina nata a cike yake, kamar dai ita da kanta ta zabi dai-dai inda take so yayi tudu da fadi, shisa babu wani abu da yayi yawa a jikin nata.

Raihana ba zata manta wani fada da sukai da ZamZam ba tace ma ZamZam din

"Katuwar banza"

Ita kuma tace mata

"Naji din, ai dai garani, kefa? Da wasu mazaunanki kamar an goge da dutsen guga"

In dai fadane su shirya tun yarinta sun sabayinshi, tunda ZamZam na da zafi, kuma ita in ranta ya baci duk abinda yazo mata fada takeyi, sai dai daga baya in ta huce, bata da girman kan bada hakuri. Amman har yau zagin nan yanayiwa Raihana ciwo, saima ta dinka riga da skirt, inta saka sai ta kalli gugar skirt din, ta kalli yanda yabi bayan nata yayi zaune, sai wani zagin da ZamZam tayi mata ya sake dawo mata

"Kai jama'a Raihana, kefa ko duwaw*n zama baki dashi"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Ranar ma biyewa ZamZam din tayi sukai sama

"Ai saiki hau sama ki fada a gyaramun"

Haka ZamZam ta dinga sheka wannan dariyar tata kamar wadda tasha wani abu. 

"Meya samu skirt dina?"

Cewar ZamZam

"Meye ma bai sameshi ba, ke bakyaji ba zaki daina saka kaya matsatsu ba, sai kinje abin gudu ya sameki ki rasa yanda zakiyi"

Dariya ZamZam tayi

"Ba sai in cire shi in yar ba"

Dariya sosai suka fara, daman aikinsu kenan, in da zasu fita tare to duk wanda zai kallesu zai dinga mamakin abinda yake ta sakasu dariya, a gefen wannan mamakin kuma zai kara da wani ne, abinda sukeyi a tare bayan komai nasu yasha bamban da juna, a yanzun dinma hijabi ne a jikin Raihana, hijabin da tadan rike da hannunta saboda kar kasanshi ya kwashe mata cakwalin unguwar tasu, mayafin da yake jikin ZamZam kuwa kamar abin tace koko haka yake, dan na net ne, dashi da babu ma kusan abu dayane, tunda bai tare mata komai ba. Wasu ma da basu san daga inda ZamZam din ta fito ba zasu rantse su kara ba tada tarbiyya ne, bata fito daga gidan kwarai ba.

Amman wannan gidan kwarai din shine zaren da yake rike da kawancensu, Raihana ta sani, sanin gidan da ZamZam ta fito ne yasa iyayenta basu datse alakarsu tun batayi wannan karfin ba. Sunje, Deeni ya dinga musu rantse-rantsen typhoid dinshu ce ta tasar masa kwana biyu, amman ya hada rigar, saura skirt din, shima zuwa dare zai karasa, tunda sassafe zaizo ya kawo mata da kanshi

"Kin fito damu munsha sanyi a banza, dinkin da ba wani na sauri bane ba, hankalinki ya kwanta"

ZamZam ta fadi tana harararta, ta bude baki zatayi magana kenan, sukaji ana danna musu hon ta bayansu, ba akan hanya suke ba, suna gefe dan ita ZamZam ma kamar zata hau bangwayen gidajen dake kan hanyar, saboda tana son kaucewa cakwalkwalin da yake kan hanyar. Jin hon din yaki karewa ta juya a fusace tana watsawa motar da mutumin cikinta wani irin kallo kamar idanuwanta da suka sha adon kwalli zasu fado, wata irin sakawa takewa kwallin, bayan cikin idon, zatayi amfani da bakar jagira ta sakashi har kasan fatar idon, sai kuma ta kewaye saman ma da bakar zagirar, haka baka taba rabata da maskara, shisa idanuwanta suke kara girma fiye da asalin girmansu. Kuma kwalliyar nayi mata kyau, Raihana ta fara sai taganta wata iri, da yake ita farace kal, irin farin nan da ake ma lakabi da kamar a wanke hannu a taba, ko mantawa tayi ta murza ido duk sai kwallin ya zazzago ya bata mata fuska.

ZamZam ta fara ganinshi, ita ta fara ganinshi, saboda ya leko kanshi ne ta window din kofar motar, wata hararar take tattarowa sai yayi mata murmushi, a lokacin batasan me ta tsaya kallo ba, sai daga baya, data nutsu sai taga ashe abinda bata saba gani bane a fuskokin maza, dimple, dimple a kuncinshi na haggu da ya lotsa sosai da wannan murmushin da yayi mata. Ita Raihana lokacin data juya, ta ganshi sai taji kafafuwanta sunyi mata sanyi kamar an dora musu abinda yafi karfinsu, da taga inda yake kallo da murmushin da yake kan fuskarshi sai zuciyarta ta kara yawan bugun da takeyi

"Dan Allaah zo mu tafi, dan rainin hankali kawai..."

Raihana ta furta tana rasa takaimamen abinda ya bata mata rai, kuma sai ZamZam din ta biye mata suka juya suka cigaba da tafiya abinsu

"Haba manaa..."

Cewar dan farin matashin daya biyo bayansu, yanda yaja kalmar karshen zaka gane ya danyi sauri kilan ya hada harda gudu kafin ya cimmusu, tunda saida ya sauka daga kan hanya ya samu wajen da yayi parking din motarshi. A wannan ranar dai, ZamZam zata rantse ta kara rantsewa idanuwanshi a kanta suke yace

"Kham, sunana Khamis"

Akwai wani abu a tattare da yanda yayi mata murmushi da yasa taji tana son mayar masa da nashi murmushin

"Fatima...ZamZam"

Labbanshi sun motsa, sauti bai fito ba, amman tagane sunanta ya maimaita, bana asalin ba, lakanin da ake kiranta dashi

"Naga kuna sauri ne, ko zaki bani lambarki kawai sai muyi magana"

Karamin tsakin da Raihana tayi ya karasa kunnen ZamZam kamar yanda ta tabbata Khamis ma yaji

"Bata da waya Malam, dan Allaah ni ki wuce mu tafi"

Ta karasa maganar tana kama hannun ZamZam din

"Ke ai kina da wayar....bani taki lambar"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Kuma ga mamakin ZamZam sai Raihana ta karanta masa lambar yana kwafewa a wayar daya fito da ita daga cikin aljihun wandon shaddar da take jikinshi. Saida ya sake yi musu murmushin nan nashi tukunna yayi musu godiya suka tafi. Raihana na fadin

"Daga ganin shi irin samarin nan ne 'yan karya"

Banda

"Uhmm..."

ZamZam bata iya cewa komai ba, haka suka karasa sukai sallama akan layi, kowacce ta nufi nasu gidan.

"ZamZam ina mukullin store din nan?"

Muryar Anty Uwani, wata 'yar uwar mahaifiyar Raihana ta kutsa cikin tunaninta. Ita ta damkawa mukullin daman tace ta ajiye mata, saboda an ajiye soyayyen nama da lemuka masu yawa da za'ayi amfani dasu washegari a ciki, ta kuma kula mutane nata shiga ana dauki dai-dai. Lalubawa ZamZam tayi cikin aljihun wandon da yake jikinta bayan ta tashi zaune, ta ciro mukullin ta bata, data koma ta kwanta sai tayi addu'ar bacci ta rufe idanuwanta tana bari tarin gajiyar da tayi ta rungumeta, kafin a hankali bacci mai nauyi ya dauketa.

*

Turaruka ne da batasan kala na nawa bane ta kara feshe Raihana dashi tun daga kasan doguwar rigarta har zuwa saman kanta, laffayane fari da yasha adon duwatsu masu kala suna ta daukar idanuwa, babu wata kwalliya a fuskar Raihanar, dan daga hoda data dan murza sai kwalli, sai kuma jambakin da ta saka, wani kalar pink ne mai duhu daya karbi farar fatarta. Kallo daya zakayi mata kagane cewar amarya ce, tun daga shigar da annurin da yake fuskarta.

"Ma Shaa Allaah...kinyi kyau, kinyi kyau sosai Ray..."

ZamZam ta fada da dukkan zuciyarta, har idanuwanta na cikowa da kwallar farin ciki, ta dauki wayarta da take kan mirrow din dakin, ta duba lokaci, sha daya saura mintina tara

"Saura minti tara"

Murmushi Raihanan tayi, ko da tana son magana ba zata iya ba, batasan ko jikinta ya nuna irin rawar da zuciyarta takeyi ba. Watanni shidda ta kwashe na saka ranarta da Khamis tana mafarkin yau, in ta rufe idanuwanta takan hango komai da zatayi daga wayewar garin har zuwa daurin auren nasu, amman wanka ma watakila da babu ZamZam data hada mata ruwan zafin ba zata san yanda zatayi ba, tunda ta tashi da asuba ta kula bugun zuciyarta ya canza, komai ma takejin ya canza mata a wannan safiyar, saima bayan wayar da sukayi da Khamis wajen karfe tara na safe, an hada mata shayi, amman yanayin da takeji ya gama cika mata ciki, sai wasa takeyi da cokalin a cikin kofin

"Kinganni sai kallon kayan da zan saka nakeyi Ray, ji nakeyi kamar mafarki nakeyi, yau dake zanyi bacci a jikina ko?"

Wata irin kunya ta lullubeta

"Dee"

Ta kira cike da kashedi, sai yayi dariya mai sauti

"Idan nace ina so inganki zaki barni? Da zance video call, amman hoto ma zai wadatar"

Murmushi tayi mai sauti

"Kabari in shirya, ZamZam zata daukeni saina tura maka"

Ya danyi jim, ta dauka zaiyi musu ne sai yace

"Babu laifi, watakila lokacin ma, idan na kura miki idanuwa, duk tunanin da gifta mun ba zanji kamar na aikata babban zunubi ba ko?"

Sunanshi ta sake kira, sunan da ta lakaba masa, sai ya sakeyin dariya shima

"Bari nima in shirya...ki kula da kanki...ana shafa fatiha akace ameeen zan kiraki"

Itace tayi dariyar kafin sukayi sallama ta ajiye wayar. Ganin ba zata iya cin abincin bane bama yasa ta tashi kawai. Sai taji wayarta tayi ringing, bata tsaya dubawa ba, tsakanin tunanin da takeyi da kuma irin yanda ZamZam take fada mata kyan da tayi har an cinye mintina goma sha biyar

"An daura Raihana, kin zama matar Dr Khamis Zanna..."

Tsikar jikinta ta tashi, a maimakon ta bashi amsa saita daga kai ta kalli ZamZam tana ce mata

"An daura, na zama matar aure ko?"

Ta karshe cikin rawar murya, abinda takeji ko zata kwana tana neman kalaman fassarashi tasan ba zata samu ba. A yau ta zama matar aure, ta taka wani matsayi da kowacce budurwa irinta take takawa. Bata san lokacin da Khamis ya kashe wayar ba, ita dai ta cire daga kunnenta ta mikawa ZamZam. Suka jiyo an rangada guda daga tsakar gida

"Alhamdulillah, alkawarin Allaah Ya cika...Raihanatu da Khamis... jama'a ku tayani guda"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Ko ba'a fada musu ba sunsan aikin Gwaggo Altine ne, da zasu leka tsakar gidan ma to zasu ga yanda take rawa tana juyi. Ba'a rufa awa daya ba tsakani akace ga Ango nan da abokanshi sunzo za'ayi hotuna. Har babban falon gidan aka shigo dasu, tare da mai hoton da aka dauko, baka ganin komai sai hasken camera dinshi. Nan ZamZam ta bar Raihana saboda kiranta da akayi, akwai abincin da aka ware na Ango da abokanshi, to kuma itace aka sa tayi wannan aikin. 

Tazo dawowa ne, su kuma zasu fice, kusan karo sukayi da Khamis, saida ta daga kai, idanuwanta suka sauka cikin nashi, hatta hular kanshi farace, sai wani irin kyalli takeyi, da sauri ZamZam ta sauke nata idanuwan zuciyarta na wani irin bugawa

"Deputy Bride"

Ya fada cikin tsokana, ta danyi gyaran murya kadan tana kokarin saita natsuwar da taji ta kwace mata

"Ango da kanshi... finally, duk mun huta ko?"

Ya fadada murmushin shi

"A'a gaskiya, ai da sauranku, ina kuka huta baku kawomun matata ba"

Yar siririyar dariya tayi

"To wuce abinka, zamu mikota zuwa anjima"

Ya daga hannunshi yana mata alamar jinjina kafin yabi bayan abokanshi. ZamZam ta kara sauke dogon numfashi

Matar mutum kabarinshi
Wani baya auren mijin wani

Duk zantukane da ba ZamZam kadai ta san dasu ba, kowanne dam adam da yayi imani, hakan ne a wajenshi

To amman, lambarta fa Khamis ta tambaya a waccen ranar
To wai me Raihana ma tace mata ya faru ne ranar farko da ta ganta da Khamis a tsaye?
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: LubnaSufyan ?
#WomenOfWords
#09035723778 (Whatsapp number)

Littafin nan na kudine da za'a iya samunshi a manhajar Arewapen a yanzun, bayan mun kammala shafuka biyar na dandano. Zai kuma zo a manhajar telegram bayan wani lokaci In Shaa Allaah.

To Aisha Abdu Gusau, with Love.

FACALA

No comments