Recent Updates

FACALA Page 8

 8

Ko lokacin da aka auro Huwaila, tazo ta samu gidan Baba Alhaji cike da yara, kamar gasar haihuwar matan nashi sukeyi a tsakaninsu. Kuma kowacce sai da tayi yara shida, ita Hajiyayye tayi bari sau biyu, sannan akwai yaran data haifa ya koma. Guda shidan da suka rayu sune, Isma'il, Habiba, Adam, Marwa, Khalid sai Autanta Ibrahim. Kuma daga Habiba harma Marwa duk anyi musu aure ne da kananun shekaru, ita Habiba ko babbar sakandiri bata kammala ba, kuma bata cigaba da karatun ba, saita rike sana'arta ta dinki, Marwa ce ma ta cigaba da nata karatun har zuwa kammala degree dinta, sai dai bata aiki, kasuwancinta takeyi, inda take siyar da gwanjo, kuma harka ce data karbeta matuka, takai matakin da sari akeyi a wajenta, tunda dila-dila ake sauke mata.

Umma itama yaranta shiddan ne, maza uku, sai mata ma guda uku, Imam, Faisal, Mahfuz, Sadiya, Ubaida, sai Auta Nasiba. Sadiya tayi aure, sai Ubaida da Nasiba da suke a gabanta yanzun. Duk da lokacin da aka auro Huwaila, ba'a haifi Ubaida da Nasiba ba, da cikin Sadiya. Zazzabin farko da Huwaila tayi a gidan Baba Alhaji sai ta dauka cikine, musamman da al'adarta ta dauke na wata biyu, sai kuma gashi ta dawo, damuwa ta shiga ba 'yar kadan ba, tarin yaran da ta gani a gidan Baba Alhaji yasa ta dauka rabonta ne a kusa, shisa ta aure shi.

Abu kamar wasa, sai gashi ta shafe shekaru biyu babu wani labari, kullum cikin fada suke ita da Umma, da ta gane babu wani abu da yake tunzura Huwaila irin ayi mata gorin haihuwa, akwai lokacin da Hajiyayye ta saka musu baki tana fadin 

"A'a Umman yara, banda magana irin wannan, kema da kika samu bafa rawa kikayi Allaah Ya baki ba..."

Saita tunzura ta cigaba da sakin maganganu, a ranar duk fada irin na Huwaila saita kasa biye mata, ta koma daki taci kuka harta ba uku lada. To ko dai da gaske bata haihuwar ne? Yanda duk Baba Alhaji yake kokarin tausarta da kwantar mata da hankali, ta kasa kwantar da hankalin nata, to shi ai ba zai gane ba, ko da bata samu haihuwa ba, batajin abune da zai dameshi, tunda yara nawane a gabanshi? Ita kuma fa? Aike wannan bata isa ta aiki yaran Umma ba, sai dai na Hajiyayye, bata taba hanasu zuwa mata aike ba, haka ranar girkinta, yanda mazan suke tayata shara, itama suna tayata.

Da yake ba abokin hira gareta ba, in ba ranar girkinta bane sai ta wuni a daki, radio ta zame mata abokiyar hira, batayi ilimin boko ba, na addinin ma ba tayi zurfi a cikinshi ba, akwai shirye-shirye na addini da akeyi, a cikin shirin ne taji addu'o'in da akeyi na neman haihuwa, ai tuni ta mike ta nufi dakin Hajiyayye wajen yara ta samo takarda da pencil, ta dawo dakin, zuciyarta har bugawa takeyi, ba rubutu ta iya ba sosai, sai kawai tayi kokarin rubuta surorin da akace ayoyin suna ciki:


Anbiya'i aya ta 89

Rabbi la tazarni fardan wa anta khayrul waarithin.

Aal Imran aya ta 38

Rabbi hab li min ladunka zurriyyatan tayyibah, innaka sami ud-du aa.

Saffat aya ta 100

Rabbi hab li minas-saalihiin.

Haka ta saka Baba Alhaji a gaba tace ya koya mata wadannan ayoyin, a ranar batayi bacci ba sai da ta haddace su. Tunda ta lazumce ayoyin nan uku, ta kuma hadasu da sayyidul istighfar da salatin Manzo SAW, sai taji wata salama ta shigeta, kamar Allaah Ya dauke mata nauyin da kirjinta yayi dangane da batun haihuwa, bawai dan taji addu'arta ta amsu ba, kawai saukin kuncin da take ciki ta samu, tunda Allaah Ne kadai ya barwa kanShi sanin adadin warakar da take tare da kowacce aya ta cikin Al-Qur'ani Mai Girma. 

Huwaila ta raba rayuwarta ne tana yawo tsakanin gidan iyayenta dana kakkaninta, iyayen mahaifinta kenan, da yake duk suna unguwa dayane a lokacin. Kakarta, macece da ta tashi ta gani da girmama addu'a, ita dai ko ciwo taji to a samo mata ruwan ZamZam ta tofa addu'a a ciki, tasha ta shafe jikinta

"Kinsan ruwane mai daraja Huwaila, kinsan tarihin samuwarshi ko? Anyi muku a Islamiyya? Nima fa wani shahararren Malami ne naji ya bayar a gidan radio..."

Sai dai tayi dariya tace mata 

"A'a Inna"

Kamar yanda suke kiranta, sai Inna ta gyara zama tace

"To bari kiji Ikon Allaah..."
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Ita kam ko a cikin bacci aka tasheta ai zata maimaita tarihin nan dalla-dalla, har yanda Inna take fadin

"Kinsan sau bakwai ta zagaya a tsakanin tsaunukan safa da marwa? Kai Hajar ba dai jaruma ba, ko da yake meye uwa ba zatayi saboda danta ba? Ta shiga rudani ne matuka..."

Wata rana kuma sai ta kara da cewa

"Manzo SAW yace ruwan ZamZam na da albarka..."

Ita dai ko sau nawa Inna zata bada tarihin nan bata gajiya dashi, wasu lokuttan ma da gangan zata takale ta da maganar, a lokaci irin wannan sai taji kewar Innar matuka, inama lokaci in ya tafi yana dawowa, ya sake baka dama, ko ta yini daya ce tare da mutanen da kake so, sai dai ai bakowanne so bane yake zuwa da samu. Sai ga Huwaila ta durfafi tofa ayoyin nan a ruwan ZamZam duk safe da yamma, tana sha, harma ta shafe cikinta. Yanda robobin suke wali a cikin shara babu wanda bai kula daga dakinta take fitowa dasu ba.

Allaah Mai kyauta da kari, sai ga Hawaila da ciki, irin cikin nan da ko an so boyeshi sai laulayinshi ya hana haka yiwuwa, kakarin amanta babu wanda baya jiyo shi da safe, sai ga Baba Alhaji ya dauke mata girki, aka sha rikici da Umma ta hakura, ita gani takeyi Huwaila karya take, babu wani ciki, balle da aka shafe wata hudu, laulayin ya tsagaita mata sosai, ga cikin bai nuna alamar akwai shi ba, duk duhun fatarta sai da ta dinga wani sheki na daban. Idan Umma ta kalleta, tana juya mazaunan nan kamar da gayya sai ta buga tsaki, a ranta tana raya watakila inda za'a tsikari Huwaila da allura, babu abinda zai hana mazaunan nan fashewa, harma wata zuciya na saka mata ko ruwan ZamZam din da ta dinga dirka ne wani ya gangara zuwa wajen ya kara cikasu fam

"Wannan da dai na ZamZam muna nan muna jiran haihuwar shi..."

Takan fadi, sai Hawaila tayi dariya

"Allaah Ya tabbatar mana idan da gaske kike Magajiya"

Lokacin da cikin ya fito ta shiga wata na shidda ne, girma yayi ba dan kadan ba, irin girman da duk wanda ya ganta in yaji watannin cikin sai yayi mata zaton ko yara biyun ne, har Hajiyayye sai da tayi magana

"Anya Huwaila ba yara biyu bane kuwa? Allaah Ya saukeki lafiya dai..."

Batace komai ba, saima murmushi da tayi, saboda tana jin kunyar Hajiyayye, matar tanayi mata kwarjini batare da wani dalili ba, Umma ce ta tayata amsawa da

"Ko dai biyun ne babu wanda zata taddo a cikinmu, ko da maza ne ta jera"

Lokacin ne Huwaila ta tankata

"Duk wanda Allaah Ya bani inaso Magajiya, ki kwantar da hankalinki, idan zabi za'a bani mace ma zan dauka, in saka mata Fatima..."

Sunan Inna kenan, ko Baba Alhaji saida ta roke shi

"Idan na haifi mace ina rokon alfarmar ka saka mata Fatima..."

Yayi 'yar dariya

"Idan namiji ne fa?"

Sai itama tayi dariyar

"Ka saka masa duk sunan da yayi maka"

Umma ta kalleta a sheqe

"Saiki ce mata ZamZam ko?"

Huwaila ta shafa cikinta

"ZamZam..."

Ta maimaita a hankali, wani kayataccen murmushi na bayyana a fuskarta

"Nagode Umman yara..."

Cewar Huwaila da dukkan zuciyarta. Kuma a ranar da ta haifi yarinyarta mace, bayan gajerar naquda, Malam ya sake mika mata ita bayan yayi mata huduba

"Na saka mata Fatima"

Ta tsura mata ido, tasan ya kamata ace tayi kawaici, ta nuna kunya, ko babu komai 'yar fari ce, amman tarin soyayyar da take yiwa yarinyar ba na wasa bane ba, da gaske 'yarta ce ta fari, tana fatan a duba shekarun da ta shafe kafin samunta, ayi mata uzurin kawaicin da ta kasa nunawa

"Fatima...ZamZam..."

Sai yarinyar ta motsa a hannunta, kamar taji abinda tace, idan bataji ba ta gane muryarta, ta gane a duniya dai babu wani hannu da zata shiga ta samu kauna kwatankwacin hannun mahaifiyarta

"Allaah Ya rayamunke, Allaah Yasa duk lokacin da wani duhu zai tunkaroki, ki samu haske kamar yanda Ya samawa Hajar da jaririnta mafita a inda ba suyi tunani ba, Allaah Yasa rayuwarki tayi albarka marar yankewa daga duniya har lahira kamar yanda ruwan ZamZam yake gudana tun daga zamanin Annabi Isma'ila..."
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Wannan shine addu'ar Huwaila, sai dai kamar kowacce uwa a lokacin data dandana dadin rike abinda ta haifa, fatan Hawaila guda dayane, ta rayu da 'yarta, ta girma, ta ga aurenta, harma inda rabo yanda ta rike ZamZam ta rike abinda ZamZam ta haifa...

Akace kowanne rai da nashi burin
Haka kuma aka sake cewa ba kowanne fata bane yake kaiwa mizani

Huwaila ta rayu da ZamZam ne shekaru bakwai kacal, kafin rai yayi abinda ya saba, ta rasu a ranar wata alhamis, bayan ciwon cikin da tayi korafinshi a safiyar ranar, ta shiga daki, ta rungume ZamZam da tayi bacci a jikinta, haka Baba Alhaji daya shiga dubasu ya sameta, dakyar aka raba hannayenta da jikin ZamZam da ta bala'in tsorata da kokawar da taga anayi, ba dan takai shekarun da zata fahimci maraicin daya maye mata gurbin rungumar Huwaila ta karshe ba. Yanda Umma ta yanke jiki ta fadi bayan an sanar da rasuwar Huwaila sai kace ta gama aikata duk wani zunubi har itama lokacinta yayi.

Amman itace farkon tsinkawa ZamZam mari saboda tayi kuskuren barar mata da ruwa a tsakar daki, ihun data fasa shiya fito da Baba Alhaji daga daki, ya kuma yi musu haukan da basu taba gani ba

"Daman ai rikon dan wani wahala ne dashi, idan ka bari ace mugunta tasa kabari ya lalace, idan ka kwabe shi nan ma ace muguntar ce saboda bakai ka haifa ba..."

Cewar Umma, Baba Alhaji da yake rungume da ZamZam nashi jikin ma yafi nata bari saboda bacin rai yace

"Har mahaifiyarta ta koma ga Allaah addu'ar albarka takeyi mata, nima kuma har in mutu abinda zai dinga shiga tsakaninmu kenan, daga yau karki kara tsawatar mata kiga idan hakan zai hanata albarka Magajiya..."

Rikici sukayi sosai, yana fada tana mayarwa, ai da alama soyayyar Huwaila tayi tsuntsuwa ta koma kan ZamZam, da bata damu ba, ganin yanda Baba Alhajin yayi watsi da lamarin ZamZam, haka suke gani a zahiri, a badini duk wani motsinta na kan idonshi, kawai daya ganta ne, kamanninta da mahaifiyarta sai su kara fito masa a fili, sai yaji komai ya kwance masa, Hajiyayye ce kawai ta kula da irin ramar da yayi, dan yaso Huwaila, yayi mata son da bai taba yiwa wata mace ba a rayuwarshi.

Fadan da sukayi na karshe harya kori Umman gida, duka ta yiwa ZamZam, har ta kuskure mata bulala a ido, shine ma ya gani, duk kashedi da tsoratarwar da Umma tayi mata, yana tambayarta me ya samu idonta, sai da ta saka shi cikin na Umma da take aika mata sakon alkawarin wani dukan akan wanda tayi mata in bata fadi abinda ta shirya mata ba sannan tace

"Umma ce ta dakeni, fitsari naji, ta hanani shigar mata bandaki, na tasheta ta rakani na waje inajin tsoro, ta mareni, nikuma nayi a kwance, shine ta dakeni"

Daga lokacin ne bata sake dukanta ba, tunda igiyar aurenta daya Baba Alhaji ya sargafe da almakashin sake dukan ZamZam da zaiyi dai-dai da datsewarta. Sai ya tattara ZamZam din ya mayar dakin Hajiyayye. Da Umma dai suka kara yin wani fadan, shima akan saka ZamZam aiki, sai ta tattara ta sama mata lafiya gabaki daya. A dakin Hajiyayyen wani irin riko ne ta samu na jeka na yika, tunda daga farko daman Hajiyayyen yayi wa magana, kanta tsaye tace masa

"Gaskiya ka ba Umman yara, kasan bana son damuwa, rikon yaron da ba naka ba wahala ne dashi...ko ka bawa dangin mahaifiyarta kamar yanda suka nema, a musulunce ma sune da hakkin riketa daman"

Ya riga yasan halinta, a karo na biyu daya tattara ZamZam kawai ca yayi mata

"Ta zauna anan, idan ina da wata alfarma da zaki iya yimun kenan"

Ba wai ZamZam din bace baya son basu, kawai gani yake da sun dauketa ya karasa rasa Huwaila kenan. A lokacin ne ta fara wata irin rayuwa mai wahala, za'a raba abinci a bata, dama-dama girkin Hajiyayye, zata ce mata

"Kije ki dauki abincinki"

Amman ranar girkin Umma, in zata wuni da yunwa, in har bataje kitchen ta duba ba, ko ta tambayi Ummar da bakinta babu wanda yake damuwa. Wanka zata curkuda abinta, mahaifiyarta macece mai tsananin tsafta, ta riga ta saba da wankan, wanki kuwa idan taga an dibo za'ayi saita dibo nata itama, haka kayanta sukayi cidin-cidin, musamman ma na makaranta a wancen lokacin, saboda suna da haske, ita kuma bata iya fitar dasu yanda ya kamata.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Randa Baba Alhaji ya ganta zasu tafi makaranta ta ware gefe, ta dayan tsallaken kamar batare take da sauran 'yan uwanta ba sai da ya dinga jin wani sanyi-sanyi na tsirga masa. Sai dai wani abune da yafi karfin ikonshi, ba wuni yake a gida ba, idan yace ayin kuma akan ZamZam dai yaga alama sai dai ya saki daga Umman har Hajiyayyen ya auro wasu matan.

Sai kawai Baba Alhaji yayi tunanin idan yana bata yan kudade da zata dinga rikewa a wajenta zai rage mata wata damuwar, amman ai babu wasu kudade da zasu maye gurbin mahaifiya, haka babu wasu kudi da zasu cike mata kishin rashin kulawar da take fama dashi. A lokacin da zata ga an hadama 'yan uwanta abinci a faranti daya, ita sai dai a ware mata nata taci ita kadai, idan akazo kwanciya kuwa, daman a dakin ita da Habiba ne, ko a lokacin ma ana gab da bikinta, a kasa takeyi mata shimfida. Sauran yaran Hajiyayye maza ne, babu wanda yake shiga sabgarta sai Ibrahim, shine yake dan mata magana, shima idan fadansu na yara ya hada, yana kwadeta sai Hajiyayye tace

"Ibrahim bakaji ko? Burinka kaga ka janyo mun bacin rai, bana hanaka shiga shirgin yarinyar nan ba? Babu ruwanku da lamarinka, babu ruwanku da ita na gaya maka bakaji..."

Irin wannan kashedin shi Umma take maimaitawa nata yaran

Babu ruwanku da ita
Ku fita harkarta

Su ta taso tanaji ana furtawa 'yan uwanta, sai kawai kwakwalwarta ta gaya mata, me zai hana ita ta fara raba kanta dasu? 

Dawowar dasu Raihana sukayi unguwarsu, aka kuma saka Raihana Islamiyya daya, aji daya da ZamZam saiya zame mata wata makafa da batasan ta jima tana nema ba, ranar farko, haka Raihana ta tsallake kowa ta zauna kusa da ZamZam 

"Sunana Raihana, kefa?"

Da tace mata

"ZamZam..."

Saita sheke da dariya

"ZamZam fa, irin wanda ake kawowa tsarabar makka?"

ZamZam ta harareta

"Sunana Fatima ai na gaskiyar, haka dai ake cemun ZamZam"

Ranar laraba ne kuwa 
Akace juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta..
Amman juma'a nawa kaddara ta zana musu? Kuma kowacce laraba ce zata alamta kyawun juma'ar?

Zahra Tabi'u tace kowanne dan adam yana da labarin bayarwa, wannan labarin nasu ne,
Ita da Raihana.




No comments