FACALA Page 10
10
"Maigida anzo kofar ruwa fa, dai-dai ina zaka sauka?"
Ya kalli gefe da gefenshi, kofar ruwa ne, tun dazun ma yaga an iso tunda yasan unguwar, gasu har sun kusa makarantar Army day, amman baisan inda zai sauka ba, kamar yanda baisan abinda yazo yi unguwar ba. Yasan abubuwa da yawa a satika hudun nan da suka wuce masa, satikan da yayi su cikin lissafi kala daban-daban. Ba zai iya tuna lokacin daya tashi yaga yana son wasa da kala ba, watakila tun daga makatin primary ne, lokacin da aka damqa masa littafin zane-zane aka kuma siya masa wannan kalar ta cikin kwali, ya bude ya zaro su har guda sha biyu a hannunshi, sai yaji babu wani abu da yake so irin yayi wasa dasu, idan ya gurza daya saiya kara wata akai yaga me zasu bashi.
"Kinga farin nan, idan da za'a hada shi da sky blue a zuba ash kadan a ciki ba karamin kyau zaiyi ba"
Haka ya cewa Mama Babba, lokacin yana aji hudu a sakandiri, za'a sake mata fenti an danyi mata wasu 'yan gyare-gyare a gidan, masu aikin fentin nan sai suka kama yi masa dariya
"Allaah Ko Faruk?"
Ta tambaya da dukkan gaskiyarta, saiya daga mata kai, a lokacin da ta cewa masu aikin fentin su tafi tare da Faruk su siyo cikon kala biyun da ya fada, sunso suyi mata gardama
"Ku dai bukatarku in biyaku kudin aikinku ne ai ko?"
Haka sukaje dashi aka siyo, ba karamin mamaki sukayi ba lokacin da wannan kalar da aka hada ta bada wata kala da basu taba ganin irinta ba, ita kanta Mama Babban bata ga kyawun dakin ba sai dare, da aka kunna farraren kwayaye, ko ina yayi fayau, ta dinga murmushi tana karawa. Ita ta fara ce masa
"Anya Faruk ba zan samo maka wajen da zaka koyi sana'ar fentin nan ba"
Shine yayi mata murmushi a lokacin, in dai zaiyi wasa da kala, kowanne irin aikine ma zai koya. Baisan ko yana cikin dalibai masu kokari idan sun dage a makaranta ba, tunda shi dai ba dagewar yakeyi ba. Bangaren Art ya tafi dan ya samu saukin haduwa da darussan lissafi da idan anayi sai ya dinga jin kamar wasu dalasuman tsafi ne ake kokarin koya masa cikin wani harshe da bai kamata a tursasa kwakwalwar kowanne dan adam fahimtarshi ba. Lokacin daya rubuta jamb dinshi kuwa, English ya cike, baisan wanne tudu da gangare aka biyo ba, BUK suka manna masa Mass communication.
Har yau kuma idan za'a yanka shi baisan ya akayi baiyi musu asarar kudaden da suka dinga biya masa ba, daga na makarantar har na kashewa da Mama Babba tafi kowa bashi su, har kasan zuciyarshi yasan saboda bayaso ya ba Mama Babba kunya ne yake dan duba hand-outs dinshi, harma wata rana idan ya samu aikin fenti ya fada musu ranakun da zai iya zuwa yayi saboda yana zuwa makaranta. Shisa har murza idanuwanshi yayi yana karawa lokacin da yaga result dinshi, wai ya kammala makarantar da second class lower, kuma CGPA dinshi har 2.85. Ya gama makarantarshi a shekarar 2012. Dan haka 2013 yayi bautar kasarshi a garin Jos, daya dawo sai kawai ya maida hankali wajen sana'arshi ta aikin fenti.
Akwai wani construction company, aikine ya hadashi da daya daga cikin partners na kamfanin, sunyi fentin wani hotel, kirista ne, amman jininshi ya hadu dana Faruk ganin yanda bashi da shiririta, sannan aikin daya kaishi shi kawai yake maida hankali wajen yi, nan suke zama su dinga hira, da yake mutumin ya karanci Architecture ne, saiya karkata kan exterior decoration, sosai suke zama su tattauna da Faruk, harma a lokacin yayi na'am da wani tayi na hadin fenti da Faruk din yayi masa a matsayinshi na wanda yake jagorantar kula da ragamar aikin, sai daga baya yazo ma suna shawarar kalar data dace da wasu wajajen tare da Faruk.
Kusan wannan aikin shine ya bude masa hanyar sosai. Yayi applying neman internship da gidan radio na Freedom. Sun karbi tayin nashi, duk da sunce ba zasu dinga biyanshi ba, ya amince ne saboda yana son ya kara kwarewa a bangaren abinda ya karanta, musamman ma da bangaren labarai yake so ya mayar da hankalinshi, ko a aikin nasu kuma bangarene da yake da challenges masu yawan gaske, sannan kuma akwai competition, idan ya samu horo mai kyau ya kware, watakila ya karama kanshi dama ta samun aiki a gaba, idan Allaah Ya amsa addu'ar Umminshi da tace
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: "Allaah Yasa suga kwarewarka su baka aikin da za'a dinga biyanka albashi..."
Shikenan, idan bashi da abinci a wajen saiya nema a wani guri. Tunda yana da bukatar duk wani kudi da zai shigo masa, dawainiyar gidansu yanzun kaso saba'in cikin dari a kanshi take, ba kamarshi ba, daga Babangida har Zaitun su din masu matukar kokari ne a makaranta. Shima kamar Khamis ya nemi Medicine and Surgery ne, sai suka musanya masa da Radiography. Sanin yanda Babangida yaso Medicine din da irin kokarin da yake dashi yasa Faruk yace masa
"Ko zaka nemi wani abin da zakayi, saika sake gwadawa wata shekarar?"
Amman ya girgiza masa kai
"Wannan dinma lafiya lau ne Yaya, Allaah Yasa hakan ne mafi alkhairi"
Har kasan zuciyar Faruk baiji dadi ba, yasan dawainiyar da za'a sakeyi daga kan jamb da sauran kananun abubuwa sune Babangidan yake dubawa, duk da shima yaro ne mai matukar kokari, ya taso taga irin gwagwarmayar da akeyi, haka ya dinga tara kudadenshi, cika masa kawai Faruk yayi, ya siyi printer, da shi da abokinshi Salim ne suka hada suka kama wani dan karamin shago a cikin makaranta, inda suka hada kayan printing, tunda shi Salim din tun daga diploma daya kammala a polytechnic bai cigaba ba, sai yafi zama a shagon fiye da Babangida, kudin da ake samu 60/40 akeyi, kaso arbain din shine na Babangida. Yana kuma rage ma Faruk nauyin dawainiyar kanshi, harma ya siyo wasu abubuwan ya kawo cikin gidan.
Sun taso babu wanda yake taimaka musu sai Mama Babba, sunsan ba mugunta ko rashin zumunci bane yake hana 'yan uwan Umminsu taimakonsu, babu halin yin hakan ne, suma kowa na fama da hidimar iyalanshi. Autar Ummi kuwa, Zaitun tace Engineering zata karanta, ita wannan burinta ma yafi na kowa, amman su duka sunsan zata iya, in dai da rai da lafiyar, tana da wannan kokarin, itace fa ta fara haddace Al-Qur'ani mai girma a gidansu kaf, tayi hakan ne a lokacin tana da shekaru goma, bata karasa cika sha daya ba. Kuma har yanzun ma Zaitun bata wasa da karatun addininta.
A cikin abubuwan da Faruk yake hangowa, inka cire kula da Ummi da Mama Babba, to yana so yaga kannen shin nan sun tsaya da kafafuwansu, sun cika duk wani buri da suke dashi, shine karshe a cikin wannan lissafin, shisa ma ya dinga ture tarin matan da suka dinga nuna masa alamun suna sonshi dama wadanda kai tsaye suka furta masa, me yasa zai bata musu lokaci shima ya batawa kanshi? Ya riga yasan bashi da abinda zai aure su, balle ayi maganar rikesu, ko kadan babu lissafin kowacce mace a cikin kanshi, idan yaga wanda suka yi masa kyau, ko suka burgeshi, da ya saka bokatan fenti a gaba, ya fara kallonsu, yana hada yanda kalarsu zata bayar yake neman wadannan matan ya rasa, sun bace masa, kalaluwanshi sun danne su.
Haka yake faruwa ko da yaushe,
Kafin ya ganta!
Daya ganta saita canza komai, sai gashi idan ya tsa brush dinshi a cikin fenti, ya dago ya goga a surface din da zaiyi aikin shi, sai ta gilma ta cikin idanuwanshi, sai ya dinga auna kowacce kala da yanda zata fito a jikin bakar fatarta. Jiya sai gashi ya shafa bakin fenti a jikin bango, ya dibi wata cream color daya watsawa baby pink ya gauraya ya shafa akan wannan bakin, sai dai wannan ai bakine kirin, ita kuma nata bakin akwai wani irin haske a jikinshi, hasken daya hadu da kowanne irin oil ne ta shafa a ranar tayi maikon da yake gani a cikin kowanne oil paint yanzun, har auna kyallin fentin nan da na jikinta yakeyi.
So yake ya sake gani, ya sake tabbatarwa, amman in ba a bisa tsautsayin daya faru ranar ba, yaushe idanuwanshi zasu sake sauka akan cinyoyinta harya kare mata kallo kamar yanda yayi a waccen ranar? Banda wannan sai me ma ya sani game da ita? Saiya tuna, yasan sunan unguwar da tace masa can zataje rannan, kofar ruwa, bai manta ba, har yanda ta furta, da labbanta da tayiwa ado da baki, ta tisa na saman sosai, na kasan kuma tayi zanen siriri, kamar kuma labban walkiya yaga sunayi, alamar ta shanshara musu mai, ko kuma idanuwanshi ne kawai?
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Ya gaji da yanda yake nemanta akan titi a duk fitar da zaiyi, ya dinga kalle-kalle kenan kamar tace masa idan ya kalla da kyau zata bullo ta wani waje, karshe dai yau sai gashi daga Freedom radio, napep biyu ya hau zuwa kofar ruwa. Gashi a kofar ruwan amman baisan ma me yazo yi ba, haka ya sauka, ya biya kudin, ya tsallaka ya sake samun wata napep din da zata mayar dashi gida. Daya kwanta sai ya dinga juyi yana rasa abinda yakeyi masa dadi, shifa wani abu bai taba yi masa tsaye a rai ba irin haka. Har tunani ya dingayi ko yar uwar matar Khamis ce, tunda a wajen bikinshi ya fara ganinta
"Idan kuma 'yar uwar Khamis dince fa?"
Wata zuciyar ta raya masa tana saka shi mikewa zaune daga kwanciyar da yakeyi, duk da idan 'yar uwar Khamis dince ba sani zaiyi ba, ko ya tambayeshi?
"Kace masa wa?"
Ya sake jin wata tambayar, sai yaja tsaki, mai sauti. Ashe baisan sunanta bama, wanne irin abune wannan? Ya sake komawa ya kwanta, wannan karin ya rufe idanuwanshi yana fatan ya samu ya runtsa. Washegari kuwa baima fita daga gidan ba sai hudu saura, a hanya ya tsaya yayi sallar la'asar. Haka kawai yaji yana so ya danyi tafiyar kasa, dan tafiya na rage masa tunani, ko wani abune yake damunshi, idan ya samu earpiece ya manna jikin wayarshi, ya samu wasu yan wakoki, saiya yanki hanya har sai yaji kafafuwanshi sun fara yi masa sanyi sannan. Dan haka a hanya ya sauka, kuma saiya tsallaka wasu shaguna ya siyi lemo, yana cikin sha ne wayarshi ta fara ringing, daya daga sai yaga oganshi ne da yake karkashin kulawarshi a Freedom din.
Daya daga yake ce masa ba saiya shigo ba yau, fita ma zaiyi, amman ya shiga da wuri gobe. Ya mayar da wayar aljihunshi, haka kawai yaji yana so ya zagaya ya shiga cikin Badawa yaga yanda unguwar take, yanayin shirun wajen yana burge shi. Haka ya taka da lemonshi a hannu, yanayin yanda rana ta lumshe yayi masa dadi matuka. Idan da wani zai saurari playlist din Faruk sai yayi dariya saboda hargitsin da yake cikinshi, waka cikin yaruka daban-daban, duk abinda yayi masa dadi saurara yakeyi. Larabci, turanci, hausa duk akwai a ciki, na hausar akwai wasu tsiraru na da da yake so, suna tuna masa lokuttan kuruciyarshi, lokacin Mama Babba na tashen kallon fina-finan ta.
Yanzun haka wata tsohuwar wakar Yakubu Muhammad mai taken Ki amsa mun kirana, ta shigo masa, sai yake tuna abubuwa da yawa, sai kuma ZamZam ta gilma masa, sai wani irin abu ya lullubeshi
Ki amsa mun kira na
Yaki abar yabo na...
Haka ya maimaita da labbanshi, ya dan daga kanshi yana kankance idanuwanshi saboda rana da ta zabi ta bude a dai-dai wannan lokacin, yanajin kalaman, da kidan da yake tashi, kasa dai sukayi suka rage kansu har suka bace masa bat, saboda wani sauti na daban daya maye masa gurbinsu, ita ya hango, tsaye, doguwar rigace a jikinta, baka, daya daga cikin ta lefen Raihana ce data bata saboda tace tayi mata yawa, tana da madauri daga wajen kugun, tayi amfani dashi ta daure, dan haka rigar ta kwanta a jikinta, jar hulace a kanta da ta danyi baya har kana iya ganin gashinta ta gaban, mayafin rigar kuma yana jikin wuyantane, wayarta take latsawa, saita kara a kunne. Baisan taku nawa yayi ya ganshi a gabanta ba, ta dago kai, ta kalle shi da idanuwanta da suka rine alamar tayi kuka.
Ta riga ta saba yin ado da kwalli, idan ta saka a cikin idon saita zagaye sama da kuma kasan idanuwan nata da bakar jagira, ta tirashi sosai. Kukan da tayi duk ya kara zazzagowa, ya ja ta wasu gefe da gefen fuskarta, hawaye ya sake zubo mata, wani abu ya fisgi Faruk, ya daga hannunshi, ya sauke, ya sake dagawa cikin kasa mallakar kanshi ya dauke mata kwallar da ta sake zubo mata, yana kallon yanda ta dan janye fuskarta bai damu ba
"Menene?"
Ya tambaya
"Me ya faru?"
Taja wata shessheka data fito da ajiyar zuciya, tana jin idanuwan Faruk akanta na kara sakata son sake fashewa da kuka
"Gidan Yaa Adam nazo...Hajiyayye ce... Hajiyayye ce ta aikoni, tun dazun...inata kira basu daga ba"
Kallonta yakeyi dai, yana so ya fahimci dalilin kukan da takeyi, dan ga wasu hawayen nan sun sake zubowa
"Me ya faru?"
Ya sake tambaya
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: "Basu daga ba, kuma bangane gidan ba, inata yawo tun dazun..."
Ta karasa maganar muryarta na rawa
"Shine kike kuka?"
Ta daga kai
"Saboda baki gane gidan ba?"
Ta sake daga masa kai tana kai hannu ta share hawayenta, kamar ta ba wasu damar shigowa. Shi dai rabon da wani ma yayi kuka a gabanshi harya manta, shisa ya rasa ta inda son ya kamota ya lallasheta yake tasowa.
"Sake kiransu, idan basu daga ba sai kizo mu tafi gida..."
Batayi musu ba, da ta sake kira sai aka daga
"Na saka caji ne ZamZam wayar kuma tana silent...kin karaso ne?"
Matar Yaa Adam din ta tambaya daga dayan bangaren, ji tayi kamar ta dura ashar, ta danne, ta kuma sake danne kukan daya taso mata. Tana jin idanuwan Faruk yanata kallonta harta gama maganar da takeyi, ta dinga leke-leke, sannan ta katse kiran
"Gidan yana ta bayan nan..."
Tace masa tana sake goge fuskarta
"In rakaki?"
Saita girgiza masa kai
"Nagane..."
Ya dan kureta da ido
"Sai anjima..."
Ta furta tana shirin juyawa
"Ya sunanki?"
Cewar Faruk, da ta juyo sai da suka hada ido sannan ta amsa masa
"Fatima... ZamZam"
Muryarta a shake ta fito, haka tajita, amman ta karasa ma Faruk ne da wani abu mai sanyi, dishewar muryar yayi masa dadi, alamar kukan da tayi ne, sai ta danyi kasa, sautinta ya dishe, akwai wani abu da suke amfani dashi a gidan radio, button ne, sai suja shi kasa, in suna editing, haka yaji muryar, kamar yaja wannan maballin
"Zan-Zan"
A cikin kanshi yayi maganar, baisan ta subuce ta fito fili ba sai da yaga yanda ta kalle shi, irin kallon sama da kasan nan, ya kuwa kai hannu ya rankwasheta
Rankwashi na biyu...
Ta dafe wajen tana murzawa
"Haka fa kace Zan-Zan..."
Dan yanda yayi maganar, yanda ya ajiye kalmar, sai ta tuna lokacin da fadinta ya shiga unguwarsu, haka kawai sai kaji in abu yayiwa yara dadi, sai suce
"Zan-Zan"
Ita dai bata taba fadi a fili ba, amman randa Ubaida ta gwada, anyi meatpie ne data gutsira saita lumshe ido irin yakai mata karon nan tana fadin
"Zan-Zan"
Yanda Umma ta buge mata baki kowa saida ya tsorata
"Wanne irin isk*nci ne wannan? Ina kikaji wannan kalmar banzar?"
Aikuwa babu ma wanda ta sakeji ya maimaita, saboda kalmar banza ce, haka Umma tace, sai shi yanzun
"Ina ruwanki?"
Ya tambaya
"Umma tace ba kyau..."
Har lokacin kanta take murzawa
"Ka rankwasheni, bana so...karka kara gaskiya"
Kashedi taso tayi masa, amman sai ya fito da sigar roko, yayi mata wani kallo, kafin ya maida hankalinshi kan kugunta, dai-dai inda ta zarge igiyar rigar nan, yana neman kullin, har saida ya gano shi, inda idanuwanshi suka bi itama take kallo, kafin tayi wani yunkuri ya saka hannu ya ja igiyar, daya kwance kullin saiya zugota gabaki daya ya cirota daga mazauninta a jikin rigar, sai gata a hannu shi, ZamZam na kallonshi ya nannade ta ya saka a cikin aljihunshi, ya kuma zaro wayarshi ya cire earpiece daga jiki yana mika mata
"Sakamun lambarki..."
Bude baki tayi zatayi magana, sai ringing din wayarta ya katse mata hanzari, ta kalli wayar tata, ta kuma kalli ta Faruk, sai kawai ya karbi tata wayar, ya katse kiran nan daya shigo, ya saka lambar wayarshi a ciki ya kira kanshi, tana kallonshi yayi danne-danne alamar saving lambarshi yayi mata. Da hannunshi yayi mata alama yana nuna wuyanshi, ta kalle shi cikin rashin fahimta, saiya nuna mata nata wuyan
"Gyalenki, ya koma saman kai"
Ya karasa yana mika hannu ya janyo mata hularta gaba, ya dan kalleta kamar maison tabbatar da hular ta zauna inda yake son ganinta, yanda ta tsaya tana kallon karfin halinshine yasa shi shiri kama mayafin nata ya rufa mata, da yake irin unguwannin nan ne shiru, musamman a irin yammacin nan da yan kasuwa suna can, haka ma ma'aikata, da sauri ta kama mayafin ta gyara ta dora a saman kanta, ya mika mata wayar, ta karba, ya dan sake kallonta ya jinjina kai, sannan yace
"Good girl"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Akwai wani abu a yanda yayi maganar, kalmomi biyu ne, amman a cikinsu taji yanda ya sallameta, yake kuma tsaye yana jiran yaga ta tafin, so take ta tambayeshi igiyar rigarta daya saka a aljihu, amman yanda ya daga girarshi duka biyun sai taji bakinta ya rufe, ta kuma juya ta tafi, da tazo yin kwana sai da ta kara juyawa, yana nan tsaye, ya kureta da ido, har sai da ta sha kwanar nan, bata daina jin idanuwanshi na biye da ita ba, saita danna wayarta, dan taga sunanshi
Faruk Zanna...
No comments