FACALA Page 2
2
Tunda akace motocin daukar amarya sunzo, aka kama Raihana data fara kuka aka nufi bangaren mahaifiyarta, sai ZamZam taji zaman dakin ya isheta, yawanci duk 'yan matan dake zaune 'yan uwan Raihanar ne na bangaren mahaifinta, sun koma gefe suna labarin da ZamZam bata gane kanshi ko da sun sakata a ciki kuwa, ballantana ma basa shiga shirginta kamar yanda ta tattarasu ta watsar. Batason wulakanci ko kadan, su wani kallon kasan ido suke binta dashi na raini. Shisa ta koma harabar gidan ta samu wata kujerar roba tayi zamanta a kai.
Sai hada-hada Aunties din Raihana sukeyi, kayan gara ne aketa fitowa dashi, tun daga kan shinkafa har zuwa maggi da gishiri, kallon kayan kawai ZamZam takeyi, ko buhun shinkafa guda hudu ne take gani, banda kuma shinkafar tuwo, kamar ana ware na iyayen miji ne, kuma a ciki ta hango atamfofi da kuma shaddoji, daman ance al'adar mutanen Katsina ce yin wannan garar. Amman abin da take ganin ne yaketa bata mamaki. Ga bokatai nan da aka nade bakin murafan da salatif
Watakila bata samu Khamis bane saboda bai dace da ita ba
Zuciyarta ta raya mata, tunda ita waye zaiyi mata wannan garar? To waye ma yake da kudin yi mata? Idan ta samu kayan daki to har azumin godiya sai tayi. Haka aka dinga fita da kayayyakin nan, tasan za'a saka a motocin daukar amarya ne. Tana nan zaunen aka fito da Raihana, mutum biyu na rike da ita, fuskarta rufe da laffayar jikinta. Yanayinta ya nuna kuka takeyi. Sai ta tashi ta koma dakin nan ta dauko wani karamin akwati da Raihanan keta jaddada mata karta bari a manta mata dashi, ko tace tama bar alhakin daukar akwatin a wuyan ZamZam.
Tana fita wajen kuwa taga motoci kusan guda goma sai daukar ido sukeyi
"ZamZam waccen motar zaki shiga, Alhaji yace ba za'a tafi da mutane da yawa ba"
Daman saida Raihana ta fada mata
"Mummy tace ba za'ayi zuga ba, tunda gidansu Dee family House ne, ba'a rasa 'yan maganganu a babban gida irin wannan, gara aje kadan kar a samu wata matsalar..."
Motar da ZamZam Anty Uwani ta nunawa ZamZam da taje saita samu akwai mutum biyu zaune a bayan motar, hakan yasa ta bude gaban ta shiga da sallama, ya amsa, sai dai inda ita din ba irin mutanen nan bace da Allaah Ya horewa jin sauti, ba lallai taji ba, motar sai kamshi take zabgawa, data zauna ta rufe murfin motar saida ta dan saci kallonshi, yasha wata bular shadda da take daukar ido, kanshi sanye da hula, amman baiyi alamar zai dago kanshi daga wayar da yake latsawa ba balle ma ya kalleta.
A biki irin hakane, kawayen amarya suke kure adaka saboda samari, abokan ango, kuma ana dacewa sosai, dan daga nan wasu suke haduwa da nasu mazajen. Kamar dai wannan hadadden gayen da yake zaune a kusa da ita, ta danyi murmushi hadi da girgiza kai kawai. Sun ma dauki kusan mintina sha biyar kafin a fara tafiya, tanata kallon titina ta gilashin motar da yake a dage gabaki daya saboda AC din daya kunna. Ita din kifin rijiya ce, banda nan unguwarsu ta Kurna, wajajen data sani zata iya kirgasu da yatsun hannunta. Tana da 'yan uwa da yawa anan garin Kano, har in da zata bude bakinta tace batasan ko ina ba, sai ayi mamaki.
Wasu ma sai sun nemi jin dalilin da zaisa tace batasan ko ina ba a garin Kano, alhalin akwai gidajen yayyenta maza dama mata da suke aure a unguwanni mabanbanta. Sai dai ai ance rayuwa sirri ce daman ko? Kuma kowa haka yake yawo da nashi sirrikan. Ance gidan a unguwar Fagge yake, amman batasan hanyar unguwar bama balle tagane inda suke, titina kawai take kallo da mutanen dake hidimarsu akai. Ta gane ko da basu shiga unguwar ba sun kusa da taga an sauka daga kan titi an fara shiga cikin unguwa, kafin kuma akayi parking. Ta dan jira, sai da taga mata biyun da suke bayan motar sun bude sun fita tukunna itama ta bude murfin motar, taja akwatin data shiga dashi da kuma yar karamar jakarta ta fito.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Unguwar take karewa kallo, akwai gidaje sosai, dan layin da alama layine da ba zaka rabashi da hada-hadar mutane ba.
Ta kalli kofar gidan da motar ta data kawosu ta tsaya, anya ma zata kirashi da gida kuwa? Ko daga tsayin katangar data zagayeshi yafi karfin ace duk wannan ne za'a dauka a dorawa gida shi kadai kuma ya iya dauka. Ko da yake ai ance family house ne, ga gate din gidan nan, baki, sai fentin kuma ruwan madara ne, yasa ZamZam tunanin yanda unguwar take a cike, ba za'ace babu yaran da zasu bata wannan fentin ba, sai wata zuciyar ta raya mata ai biki akeyi, watakila an sabunta fentin ne shisa ta ganshi qal. Saida gabaki daya motocin suka jeru tukunna aka bude musu gate din, sai taga wasu daga cikin motocin harda wadda aka saka Raihana sun danna kai cikin gidan, ta danyi karamin tsaki tanajin daman basu sauko ba suma an shiga dasu ciki.
Haka suka taka da kafafuwansu, tana rike da akwatinta, sai da ta shiga tukunna ta gane dalilin girman katangar nan. Ita a fina-finan Hausa ta fara ganin estate, sai kuma wani Yayanta da yayi aure, shima a estate ya kama haya, amman sau biyu ta taba zuwa, lokacin bikin, sai haihuwar da matarshi tayi sukaje suna. Kuma ZamZam taga gidajen duk gininsu iri dayane, duk da wasu sun dan sabunta fentinsu, ko sun karama nasu wata kwalliyar daga waje, duk da haka zaka gane ginin dai dayane. A maimakon nan da suka shigo, gidajen ba iri daya bane ba, wasu sunfi wasu kyau sosai, wasu ma kamar bai kamata ace an jerasu a waje daya da sauran gidajen ba balle har a suturtasu da katanga daya, gidan Zanna kenan, kamar yanda 'yan unguwa suke kiranshi.
*
Alhaji Zanna, bahaushe ne dan asalin cikin kwaryar garin Kano, sunanshi na gaskiya Ahmad ne, daya guda daya Tilo a wajen iyayenshi, dan basu samu rabonshi ba sai da girma ya cimmusu, dan lokacin ma sun cire rai da samun haihuwa. Ya taso cikin soyayyar da bata hana masa kadaici ba, da yake danginsu ba masu yawan zumunci bane ba, gashi babu wasu sa'anninshi maza a dangin da yaga iyayenshi na zumunci dasu, lokacin duk sun girme masa, sai ya kara janye jikinshi. Kuma shi mutum ne da bashi da hayaniya, sannan ya riga ya tashi da burin da baka raba duk wani matashi dan asalin Kano dashi, neman na kai, kowa zaiyi shaidar mazan Kano basu da lalaci, sun yarda da neman na kai ko yayane, a madadin hangowa kanshi wani matsayi a karatun boko da ayyukan gwamnati, mafarkin Ahmad kasuwanci ne, irin kasuwancin da zai sama masa rufin asiri mai yawa.
Yana son ya samu kudine, dan inya hango gobenshi, yana hango kanshi ne da mata hudu, matan da zasu tara masa yara masu yawa, yanda zuri'arsu ba zata kare daga kanshi ba, kuma yaranshi ba zasuyi irin kadaicin da yake dashi ba. A lokacin da yake da shekara goma sha biyar ne, makotansu da 'yan garin Maiduguri ne suka samu ziyarar wasu daga cikin 'yan uwansu, harda Kanin maigidan dashi zaiyi shekaru ashirin a wancen lokacin, saiya fito kofar gida, kan dakalin da sanyin safiya, yana dinkin hula. Kawai yanda kwalliyar dinkin yake fitane ya fara burge Ahmad, har ya soma zama yana kallo, da kuma yaji irin alkhairin da ake samu da sana'ar dinka hula, sai abin ya shiga ranshi, ya nemi da yanaso ya koya masa.
Tunda ya cewa wani a cikin abokanshi daya nemi yazo suje wata unguwa
"Nifa babu inda zanje, gara na zauna na gwada abinda na koya na dinkin hular nan, sallar bana sai dai kaganni da Zanna bukar dina..."
Sai kuwa ya sheke da dariya, ya kuma fadawa sauran abokansu na cikin unguwa, ya zamana duk inda zasu ga Ahmad sai suce
"Zanna Bukar ne"
Har asalin sunanshi ya fara bacewa, suka kuma takaita shi zuwa Zanna din, maimakon hakan ya sage masa gwiwa saiya kara masa karsashi, in ka duba hannuwanshi kuwa duk sukar allura ne, bai damu ba, kamar yanda ya fadane, hular da yayi sallar idi da ita a babbar sallar shekarar, wadda ya dinka ce. Labarin Ahmad Zanna ba irin labaran nan bane da za'ayi amfani dasu a karfafa maka gwiwa, ace maka ai daga fara dinkin hular nan komai ya bude masa, kasuwancinshi ya bunkasa.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Yasha wahala, musamman bayan rasuwar mahaifinshi, da kuma doguwar jinyar da mahaifiyarshi tayi, dangi duka suka kara nesa dasu, babu wani mai dubasu sai wata abokiyar wasan mahaifinshi, Kaltume, itama ba wani hali take dashi ba.
Dan anyi mata aure ne tana da shekaru sha uku saboda maraici, anan kauyen Badume da yake garin Kano, shi kanshi Ahmad din yasan ya girmeta, amman haka zatazo dubasu da buhunta mai dauke da tsarabar kauye kala-kala, idan zata koma kuma yace zai bata kudi sai tayi murmushi tace
"Amadi kenan, da kudin motata...kai dai ka kara hakuri, komai mai wucewa ne"
Amman a cikin komai din nan, da ya tashi wucewa sai ya tafar masa da Innarshi. Kaltume bata fasa zuwa dubashi ba, bata kuma fasa zuwa da duk wani abu da Allaah Ya hore mata ba. Ya sha wahala, yayi fadi tashi, kuma da yake akwai rabon arziki a kaddararshi, sai Allaah Ya saka masa nasibi a wannan sana'ar dinkin hular. Gidan nan nashi na gado da yake a unguwar fage, anan yayi aurenshi na farko da Huwaila (Mama Babba). Saida sukayi shekara hudu da aure, ko batan wata bata tabayi ba sannan ya kara aure, ya auro Hajiya Salma (Gwaggo).
A lokacin da ya aurota, arzikinshi ya fara habbaka sosai, dan harya kara siyan wani gida kusa da nashi ya hade, kuma watanta biyu ta fara laulayi, macece mai iyayi da rashin son zaman lafiya. Danma Mama Babba na da kawaici, haka Gwaggo da danginta sukaita sintiri suna yada mata maganganu. Jikinta ma ya mutu ne data fara da haihuwar mace. Amman Zanna bai damu ba, murna yakeyi yana karawa kamar anyi masa albishir da kujerar makka. Katon sa aka yanka na suna, wannan rawar kafar ce ta dawowa da Gwaggo karsashinta. Gwarne tayi, ta sake haihuwar mace.
Hankalinta ba karamin tashi yayi ba da Zanna ya rungomo aure, dan saita dauka da namijin da bata haifa bane ba, lokacin taki kwantar da hankalinta, har saida saki ya gifta tukunna ta dan natsu. Ya auro Madina (Ummi). Kusan lokaci daya suka sake samun ciki da Gwaggo. Suka kuma haifi maza. Har lokacin Mama Babba batayi ko batan wata ba, danma Ummi tazo mata ba kamar Gwaggo ba, har daki take zuwa tana kai mata yaron data haifa, in ba yaji yunwa ba, shima tana gama bashi yasha take sake kaishi, wani abu da ya siyawa Ummi daraja da kima ba a wajen Mama Babba ba, harda ma Zanna.
Ya rufe da mata ta hudu, data zama cikon mafarkinshi, Saddika (Hajiyayye). Lokacin kudi kuwa sunayi da Zanna, ya sauke farali shida Mama Babba. Haka kuma ya dinga daukar sauran matan yana zuwa dasu. Gida kuwa cikin unguwar nan, inya kyalla ido akai yaga akwai damar da zai shigo dashi ya hade da nashi, sai yayi maka tayin da kudin zasu saka ka siyar masa
"Wai duk me zakayi da wannan gidan ne?"
Mama Babba ta taba tambayarshi cikin raha
"Yarana nake siyarwa, bana fatan ko bayan raina wani a cikinsu ya fita yace zaiyi nashi ginin, duk iyali inaso su zauna waje daya yanda ba zasuyi kadaici ba, kuma zumuncinsu zai karu"
Shi Alhaji Zanna, a wannan lokacin, fatan kawai yayi, burinshi kawai yake hangowa, baiyi tunanin wani abu zaiyi karo da wannan fatan ba balle yayi addu'a akai, addu'ar da inta amsu, watakila da ta canza abubuwa da yawa a gaba...!
Lokaci daya Mama Babba suka samu ciki da Hajiyayye, lokacin haka Gwaggo ta dinga sakin maganganu tana fadin
"Ayi dai mugani in tusa zata hura wuta..."
Dan kishi takeyi da kowacce mace a gidan, musamman ma Mama Babba, babu wanda yake biye mata sai Hajiyayye, har dambe suka taba kwasa, ita Gwaggo bafullatana ce, siririya, sai neman rigima, Hajiyayye kuwa dirarriyar macece, ta dinga daga Gwaggo tana damfarawa da kasa, Mama Babba ce ta raba fadan, Ummi take ce mata
"Meya kaiki? Ai da kin kyalesu tunda Allaah Ya kawo mana mai saita mata zama"
Sai fadan ya so ya koma kan Ummi, ta shige daki ta rufo kofarta. Yanda Alhaji Zanna ya hangowa kanshi tarin yara kamar talatin ko sama da haka sai bai samu ba. Mama Babba yaranta biyu, Asaad da Hidaya. Inda Gwaggo take da guda biyar, duk da har zuciyarta taso ace mazan ne ta jera haka, Badriyya, Jawahir, Khamis, Laila, sai Auta Maryam da taci sunan mahaifiyarta suna kiranta Ihsan.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Ita Ummi yaranta uku ne, Umar da suke kira Faruk, Ahmad (Babangida), Aisha (Humaira). Hajiyayye nada guda biyu itama, Jafar da Iman. Jimillar yara goma sha biyu kenan, maza biyar, mata bakwai.
Hankalin Alhaji Zanna bai kwanta ba saida yaga ya siyi gidaje a gefen haggu da damanshi, dama wasu a bayan wadannan gidajen, yagansu guda goma rasa, sai a lokacin ne kuma ya ballo wani sabon aikin, na katange gidajen daya mallaka kamar yanda ya taba ganin wasu gidaje a garin Abuja da kasuwancinshi ya kaishi. Wani abu daya zama bako a gurin mutanen unguwar, ya kuma janyo surutu mai yawa daga wajen Gwaggo, tunda takardun gidan ya kira shaidu, Malaman unguwa, mai unguwa hardama wani alkali mazaunin nan Fagge, akayi shaida, da takardu ya rubutu sunayen yaranshi maza yana mallaka musu gida dai-dai daga cikin wadannan gidajen, dan a lokacin ma ya kara raba inda matan suke ya zamana kowacce nada nata sashin, suma saiya mallaka ma kowacce nata sashin.
Rigima Gwaggo ta tayar ba 'yar kadan ba, rigimar Ummi da taci gidaje uku kenan, na yaranta biyu, ga bangarenta, sai kuma na bangaren Mama Babba da yafi na kowa girma. Nan ma saida ya korata gidansu, baiyi saki bane saboda darajar yaran dake tsakaninsu, aka lallaba ta dawo da fitina shakare a zuciyarta. Babu dai yanda zatayi da wannan rabon da Alhaji Zanna ya riga yayi tunda ranshi, akwai wani karamin gida daga can gefe da sai daga baya suka san na Kaltume ne, dan mijinta ya rasu, bata kuma taba haihuwa ba, kamar dai yanda Alhaji Zanna ya fahimta daga baya, wannan matsalar rashin haihuwar haka yake yawo a dangin mahaifinshi, wanda suka haihun zaka samu yaran basu da yawa. Itama mallaka mata gidan yayi da shaidu da komai, dan bayaso ko da bayan ranshi Kaltume ta wulakanta, shi din mutum ne da baya manta halarci.
Wanda yasan Alhaji Zanna, mutanen da sukai rayuwa dashi, wanda suke da rai har zuwa yanzun, zasu bada labarin irin tashen kudin da Alhaji Zanna yayi, zaku ma su kara da bada labarin tsananin jinyar da yayi fama da ita, jinyar da kowa da abinda ya dinga fada akanta, haka aka dinga daga wasu a cikin qaddarorinshi ana siyarwa, saida ya cinye kusan komai daya tara kafin rasuwarshi, shisa lokacin da aka tattara dan abinda ya rage aka raba, babu yawa. Wannan shine takaitaccen tarihi Alhaji Zanna da ahalinshi.
*
Kuma mamakin ZamZam ya dinga karuwa ne da ganin gidaje goman nan da tarin bambancin da yake tsakaninsu. Haka kawai, sai idonta ya tsaya kan wani gida da fentinshi ya tsufa har ya fara bambarewa, ga busasun ganyayyaki nan a kasan gidan, kamar an ware shine gefe, kamar duk tarin canje-canjen zamani bai riske shi ba, gidan yayi daban da sauran, yayi gefe shi kadai
Ko waya fara zama a cikin gidan?
Ta tambayi kanta
Ko wa kuma zai kara zama a cikinshi?
"Ta can nefa gidan, kikai tsaye anan"
Wata ta da bata ga fuskarta ba ta fada mata, sai taja kafafuwanta da wannan akwatin, haka kawai ta sake juyawa ta kalli gidan nan, wannan karin tare da kaddarar da ba zata iya kaucewa ba...!
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: LubnaSufyan ?
#WomenOfWords
#09035723778 (Whatsapp number)
Littafin nan na kudine da za'a iya samunshi a manhajar Arewapen a yanzun, bayan mun kammala shafuka biyar na dandano. Zai kuma zo a manhajar telegram bayan wani lokaci In Shaa Allaah.
To Aisha Abdu Gusau, with Love.
FACALA
No comments