FACALA Page 7
7
Sai da taje gida sannan ta tuna duk saurin da takeyi wajen tahowa da dadin labari, a kitchen din Raihana tabar ledojinta, sai dai mamakin rankwashin da Faruk yayi mata saiya danne takaicin mantuwar. Ta riga ta saba dole sai tayi wanka da daddare take iya bacci, duk kuwa tsananin sanyin da akeyi a gari, ko bata samu ruwan zafi ba saita watsa na sanyin
"Sai kace wankan tsafi, Allaah Ya kyauta miki ke kam"
Haka Umma ta taba ce mata, lokacin ana wani mukumukun sanyi, ta fito wankan tana makyarkyata kamar zata shide, sanyi ma bai barta ta tanka ba, ko da babu sanyi ba zatayi magana ba, dan Umma ta tara mata kaf 'yan gidan tace ta zageta ba wani abu bane ba, shisa ta ruga daki ta shige cikin bargo. To yau ma tana idar da sallar Ishai, tayo wankanta, saida ta kwanta taji yunwa, inda ta taho da abubuwan da Raihana ta bata, babu abinda zaija mata fita neman wani abu, tunda harda wasu manyan biskit ta bata, kitchen din ta nufa, taga kular da ake kwashe abinci a ciki, tasan girkin Umma ne, kowama sai abinda ya gani, tana budewa taga dafaduka ce ta manja aka wargatsa musu, ta samu filet ta diba.
Ta wuce dakinta, ta dauko kofi, tana da milo dinta da madara tunda idan Baba Alhaji ya bata 'yan kudin kashewa saita siyi kananun abubuwan da tasan ko ya kawo bata da rabo a ciki, an rabane tsakanin Umma da Hajiyayye, kowa kuma ya kwashe nashi ya shige dashi bangarenshi ya adana daga shi sai 'ya'yanshi. Shayin ruwan sanyi ta hada, dan dai ta samu abinda zata kora shinkafar nan kar ta dinga shaqareta, amman tayi yaji, ita kuma bata son yaji, ta saka shinkafar a gaba tana kallo, sai taji ana kwankwasa mata kofa
"Waye?"
Ta tambaya
"Dalla nine, ki kama kofa ki dinga garqamewa kamar kin ajiye wani abu a dakin"
Murmushi ya subuce mata da taji muryar Ibrahim
"Ibro nawa..."
Tayi maganar tana bude kofar da turata tayi daman, shima murmushin yakeyi mata
"Shine babu sanarwa?"
Ibrahim Yayantane da tsiran shekara uku a tsakaninsu, yana makaranta a garin Zaria, yana aji biyu ne wato 200 level, kuma duk a cikin 'yan gidan shine suka fi shiri, dan babu wani da yake shiga harkarta kamarshi din
"Ai nima bansan zanzo ba, kawai Zariar ce naji ta isheni na gudo gida..."
Sai ta karayin dariya
"Daman da nazo Hajiyayye tace kin fita, yanzun kuma na shigo zan fita kallon ball ne nace bara mu gaisa"
Taji dadi kuwa har ranta
"Dan Allaah zaka taimaka ka tahomun da biredi idan zaka dawo?"
Maganar ta fito ne a darare, saboda duk shirin da suke da Ibrahim, shi mutum ne kamar mai iskokai, abu kadan yake birkitashi, yanzun yanzun kuna dariya da juna, minti kadan saiya hautsine ka rasa gane me kayi masa daya birkitashi
"Kai, bafa yanzun zan shigo ba gaskiya, bara na dubo miki shagon Halilu..."
Kafin ma ta numfasa ya fice, daya dawo sai gashi da sabon biredi mai yanka-yanka, harda kwai ya hado mata dashi guda hudu, da tayi masa godiya sai ya daga mata kai yana ficewa abinshi. Sai itama ta koma dakin, ta samu waje ta ajiye kwan, biredin ta gutsira tasha da sauran shayin data hada, sannan ta dauki wayarta ta kwanta a gado, batasan ma ya akayi ta shiga silent ba, akwai tarin kiran da Raihana tayi mata, sai kuma sako tana fada mata mantuwar da tayi
"Dee ba wani lokaci yake samu ba, amman zan rokeshi ya kawo miki kayan gobe idan Allaah Ya kaimu, saura kisa wayarki a silent"
Tayi dariya kawai batare da tayi replying sakon bama, kwanciya tayi da nufin bacci, amman sai tunanin Faruk da abinda yayi mata ya dinga zagaye a cikin kanta, sai kuma wai take komawa baya a cikin wannan tunanin tana gwada abubuwan daya kamata ace tayi amman batayi ba. Yanda ta tashi sallar asuba da nauyin da kanta yayi ne abinda ya tabbatar mata da ta jima kafin bacci ya dauketa daren jiya. Saida ta fara gabatar da salloli biyu na nafila, sannan tayi asubar, duk baccin da takeji kuma batayi ba saida tayi azkar dinta, ta karanta shafuka biyu daga Al-Qur'ani mai girma kamar yanda takeyi duk asubar duniya, ko da bata cikin tsarki saita karanta abinda ya sawwaka daga haddar da take da ita, ta kumayi azkar.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Bacci tayi har wajen tara na safe, lokacin da ta fito tsakar gidan bata ga kowa ba, sai ta wuce bandakin tsakar gidan, wanda ita kadai take amfani dashi, sai kuma baki idan anyi, dan haka ma duk kayan wankanta suna ciki, idan zata fita bata manta ba saita kwashe kar ayi baki a taba mata, ko idan ta ga bakin saita dauke. Wanka tayi ta fito ta koma daki, ta gama shiryawa tsaf cikin wata doguwar fitted gown, in kaganta saika rantse wani wajen zataje, babu kuma inda zata. Kitchen ta wuce, tunda taga manja soyayye a wata karamar tukunya tasan cewa alale akayi, kuma babu alamar an ajiye mata. Wani abu da ta kasa sabawa dashi yazo ya tokare mata makoshi, kwalla ta taru cikin idanuwanta.
Ta koma daki ta dauko kwanta na jiya, shi ta soya, duk sanda zatayi amfani da gas saita yiwa Yayansu Isma'il addu'a daya 'yantasu daga amfani da itace, duk da ana kunna gawayi har yanzun, amman cylinder manya guda biyu ya siyo, haka bai taba gajiya da cika musu da gas ba. Ta dafa ruwan zafi ta samu kofi ta juye ta fito daga kitchen dinne taga Umma
"Ina kwana..."
Ta gaisheta cikin karamar murya
"Hamshaqiya mandiya an tashi kenan...ke kam dai Allaah Ya fisheki zaman aure, dan tabbas akwai kallo"
Umma ta karashe maganar tana tabe bakinta
"Ko dan rayuwar da uba*ki ya zaba miki kenan ai...saiku karata"
Wucewa ZamZam tayi, data shiga dakinta ta zauna ma saita dinga juya cokalin nan cikin ruwan zafin batare data saka masa komai ba, gabaki daya abincinma ya fice mata daga kai, batasan yanda ake so tayi a cikin gidan daya kamata ace ta samu sakewa da walwala fiye da ko ina ba. Kalaman Umma kenan kullum, ta haddace su tun tana da karancin shekaru, har yanda take caccanzasu, duk da ma'anar iri daya ce, kawai dai kalaman na shigarta ne a mataki-mataki na hankalin da takeyi. Ai har ranar data fara fada mata ma bata manta ba, saboda wani kallo ne tayi ma ZamZam din, kallon da yasa taji kamar ta watsa mata ruwan sanyi, sannan ta kalli Baba Alhaji tace
"Mun barta Alhaji, in dai ZamZam ce ta mike kafa ta zauna ta huta kamar yanda kake so, in taje gidan wani sai muga ko wannan zaman zai fisheta"
Kalaman ne sukayi mata kama da baki, shisa ta kasa mantasu, kuma har yanzun din sai taji kamar mugun fatane Umma takeyi mata, akan gidan auren da ko shigarshi batayi ba, to a yanda take gani, take kuma jin labari, auren da kanshi wata makaranta ce mai zaman kanta, kuma matsalolin cikinshi suna da yawan da duk addu'ar alkhairin da ake binsu da ita wasu matan a jigace suke fitowa daga cikinshi, balle kuma ita da take jin yanda kowa yake hango mata karewar aurenta tun kafin ya fara, wacce irin rayuwace wannan?
Dakyar ta samu ta tura kwan bayan ta goge hawayenta, saita fita da kofin, ruwan ya riga ya huce, dan haka ta zubar dashi ta mayar da kofin muhallinshi, ta fito ne taci karo da Ubaida zata tafi makaranta, cikin fararen kayanta, ganin ZamZam din yasa ta wani murmushi, musamman da taga yanda take kallonta
"Umma saina dawo..."
Tayi maganar cikin wata murya, itama Umman murmushin take
"Allaah Ya bada ilimi mai amfani 'yar albarka. Sai kin dawo"
Itama ZamZam din murmushi tayi, irin murmushin nan da ake cewa yafi kuka ciwo. A maimakon ta koma dakinta, saita wuce falon Hajiyayye, tunda taga da wuta, da ta zauna tunani ya haye mata ita kadai a dakin, gara taje ta zauna tayi kallo, tasan a dai-dai wannan lokacin Hajiyayyen na kallon wani shiri ne na documentary da ake gabatarwa a tashar Al Jazeera. Itama kuma tana son shirin sosai
"Ina kwana"
ZamZam din ta gaishe da ita, tana samun waje akan kafet ta zauna, tanajin yanda rigarta ta matse mata ciki, ta gyara zama yafi a kirga, sannan ta dan samu sa'ida
"ZamZam yanzun nake zancenki a raina, kinga an fara shirin nan, naga yau indiyawa ne, an dai nuno wata tsohuwa tanata bayani, aka kuma nuno wasu yan mata da aka dishe fuskokinsu, anata yanke musu gashi, kiga nan ma gashin ne aketa wanke shi ana gyarawa..."
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Dariya ZamZam tayi a hankali, Hajiyayye akwai son kallon abubuwa irin wannan, amman da yake ba fahimtar turanci takeyi ba, shisa itama tanaso ZamZam din ta shigo, ko film ne akeyi kam, zata maida hankaline ta natsu, ZamZam na fassara mata abinda ake cewa, kusan zatace wannan abin na daya daga cikin abubuwan da suka sama mata sassauci a wajen Hajiyayye, tunda ko a shekarun baya ma, yaran Hajiyayyen babu mai hakurin amsa tarin tambayoyinta sai ZamZam, ita kanta tanajin dadin foundation na makaranta mai kyau da suka samu daga matakin Nursery harma karamar sakandiri.
Alhaji Haruna da kowa yafi sani da Baba Alhaji, asalinsu yan garin Katsina ne, karamar hukumar Mani, kasuwancine ya kawo kakanninsu garin Kano, har suka haifi iyayensu, suma kuma aka haifesu anan Kanon. Hajinshi bata sauke farali bace ba, ana masa lakabi da Alhaji ne saboda haihuwarshi da akayi ranar Arfa. Yaran 'yan uwa kuma su suka fara lakaba masa Baba Alhaji, shine sunan yabi shi har nashi yaran suke kiranshi da haka. Baiyi karatun boko mai zurfi ba, asalima ko sakandiri bai gama ba, tunda ya fara zuwa koyon sana'ar kafinta a wancen lokacin, ya kuma fara kama 'yan canji, sai yayi watsi da batun karatu ya rike sana'ar gam, har Allaah Ya saka masa nasibi a ciki ya bude dan nashi wajen acan unguwar kurna, kan titin babban layi.
Aurenshi na farko da Balaraba, ba aurene da zai kira na soyayya ba, tun yana da shekaru bakwai a duniya aka bashi ita, yar aminin mahaifinshine, abin kamar wata almara, itama an haifeta ne a ranar Arfa, sai dai a madadin Hajiya, ake kiranta Hajiyayye saboda a bambanta tsakaninta da kakarta da ake kira Hajiya a wancen lokacin
"Ai kuwa Alhaji ya samu mata"
Haka mahaifinshi ya fadi, shikuma aminin nashi ya amsa da
"In Shaa Allaah ko mutuwa nayi Balaraba bata da miji sai Alhaji"
Haka wannan alkawari ya cika tare da kaddarar yaran da suke tsakani. Kowa kuma yasan yanda sana'r aikin kafinta take a wancen lokacin zaisan akwai samu a cikinta matuka. Hakan ne yasa Alhaji Baba karo aure, ya auri Magajiya da yaran suke kira da Umma. Bayan shekara kusan goma da wannan auren, ya kammala ginin gidan da suke zaune a cikinshi a yanzun. Gini ne da yayi shi dai-dai da wancen zamanin. Dan lokacin yaje gidan wani abokinshi da akeyi yaga yanda akayi musu bandaki a tare da dakunan nasu, abin ya dinga burgeshi. Sai shima akayi masa irin wannan tsarin, duk da nashi da aka hade falo da dakin bacci akayi bayin, sai kuma akayi wasu falle fallen dakunan. Gini ne wadatacce, kuma wadannan dakunan masu bandaki a ciki, guda uku yayi, da nufin daya ya zama nashi.
Wanda haka akayi, inda Hajiyayye ta dauki dakuna biyu falle-falle ta hada da nata, abinda ma yaso tashin tarzoma saboda Umma tace sam bata yarda ba, sai dai itama a hada mata da falle biyu. Ta hakura ne da yace itama Hajiyayyen dayan dakin zai zama na samarin gidan ne. Sai dai yanda ka tsara rayuwarka hasashene da fata kawai kakeyi akan rayuwar ta tafi da wannan tsarin, sai abinda yake faruwa da mutane da yawa ya faru da Baba Alhaji, wato kaddara ta fito da nata tsarin, ta rungumeka tsam, kuma ko da bakaso ba haka zakayi mata maraba.
A lokacin da in za'a ce ma Baba Alhaji ga mace sadaka ba zai karba ba, bawai dan bayaso ba, tunda ai zuciyar tashi ma da aka halitta masa ita, anyi tane da wajajen da zaiso mata hudu, su rayu a ciki batare da wata ta takurawa wata ba, wasu ma sun cewa wajajen nan sunfi hudu idan akayi duba da mazan da suke da dabi'ar auri saki, wasu kuma sukace ina ruwan kwadayi da so? Dalilin Baba Alhaji shine nauyin iyali da yake kanshi, da kuma yanda rayuwar ta sauya masa, saboda a lokacin da mutane suke kokarin koyon yanda zasu sabunta ayyukansu suyi dai-dai da zamani, shi kamar wanda aka rike, ya kasa yin wannan yunkurin, haka wanda suka sameshi a wajen nan suka dishe nashi hasken, ciki harda yaran da a karkashinshi suka koyi aiki.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: A lokacin ne ya hadu da Huwaila, sunzo siyan gado, da sukace na hannu suke so sai aka rakosu shagonshi. Ya dauka a wannan shekarun ya girmi soyayya, to tun zamain kuruciya, mata wanne kalane baigani ba, sai gashi ya kafe Huwaila da ido yana jin wani abu mai kama da rabo yana fisgarshi a kanta. Da haduwarsu, da auren, komai ya farune cikin watanni uku, da yake Huwailar ba budurwa bace ba, tayi aurenta na farko, mijin Allaah Yayi masa rasuwa bayan shekaru biyar, kuma basu samu rabo ba, dan ance shine baya haihuwa shisa ma matarshi ta farko ta rabu dashi.
A wannan auren Hajiyayye bata bashi matsala ba, karamin yaki sukayi shi da Umma, balle ma daya fita daga bangarenshi, ya koma falle dayan daya rage extra, wanda ta fara ajiye tarkace a ciki, ya barwa Huwaila nashi bangaren, tun bata ganta ba take jin kishinta na gaske. Lokacin data shigo, taso ta gallaza mata ne, bawai kiba Huwaila take dashi ba, wani irin jikine da ita mai daukar hankali, kuma kamar da gayya take yawo a cikin gidan tana juya musu mazaunan da Umma ta kira dana banza.
"Mazaunai dai na zama, Allaah Ya horewa kowa"
Haka take yawan fada, dan ita dirkekiya ce, tana da tudun kirji, amman mazaunanta a lomake suke, a wani fada da sukayi. Huwaila na da wata fuska da inka kalleta zaka rantse ka sake rantsewa ko dan yatsa ka saka mata a baki ba zata ciza ba, saika gwada ne zata gutsire shi ta taune har kashin. Gashi ta kware a kissa, bata taba kai kara, kome zai hadasu da Umma, ita Hajiyayye daman ta kama girmanta, tunda ta kula Huwaila ba kanwar lasa bace ba, sannan a dake ba zata daku ba, dan wani fada da sukayi da Umman, Huwaila tace mata
"Haka dai zaki ganni da kirata ki barni, kurwata kur wallahi, mata sai hassada, saboda ke kinganki kamar an tashi kwado tsaye...."
Haka Hajiyayye ta shige kuryar daki, ta dinga hasashen yanda kwado zai kasance idan ya mike tsaye, tayi dariya ba yar kadan ba, shi kanshi Baba Alhaji da aka kai rigimar gabanshi, ba karamin karfin hali yayi ba wajen danne dariyarshi, musamman da yaga yanda Umman ta cika tayi fam...
No comments