FACALA Page 6
6
Kafafuwanshi yake dagawa kamar wanda bayason taka kasar, daga nesa wasu zasuyi zaton ko irin takun nan yakeyi daya baya dayan, na matasa 'yan gayu, musamman da yake akwai wata katuwar jakar goyo a bayan nashi, idan ka matso kusa ne zaka gane gajiya ce a tattare dashi, irin gajiyar nan da take saka tunanin gatan da zaka yiwa jikinka inda zaka samu baccin kwana uku batare daka farka kayi komai ba, idanuwanshi har rage girma sukayi saboda baccin da yake cikinsu. Tare suka taho da abokan aikinshi, sai suka ajiye shi daga can kan junction, ya kamata ace ya samu abin hawa ne da zai karaso dashi har kofar gida. Da yake yamma tayi, duk napep din da zata taho sai ya ganta a cike da mutane, ko kuma da mutum a ciki, ba zai yiwu su shiga dashi lungu ba, ganin tsayuwar ba zatayi masa ba saiya tako.
Kamar ance ya daga kanshi, saiya hangota, tanata gyara mayafin da yayi masa kama da abinda Ummi take tace kunun aya dashi, garama wancen abin, idan za'a warware kullin da Ummin tayi masa ta gefe da gefe zaifi mayafin ZamZam girma, kuma ita daga inda yake ma yana hango bula-bulan da take jikin nata mayafin. Skirt din da ta saka kuwa saika rantse a jikinta aka dinka shi saboda yanda yabi ko ina yayi luf, ga idanuwan Faruk sunga skirt din nan, sai kawai kwakwalwarshi ta cire masa shi, sai wannan hoton na rannan ya dawo masa, jan wandonta, yanda ya kwanta akan bakar fatarta, ya runtse idanuwanshi, a maimakon jan wandon sai ya hango kalar sararin samaniya, kalar da tafi daukar hankalinshi a duk cikin kaloli, saima yaga yanda kalar zata haska a jikinta.
Babu shiri ya bude idanuwan, suka sake sauka akan ZamZam da take tsaye a bakin titin nan, kanshi yake girgizawa yana tunanin abinda yake damunshi da wannan tunanikan, ko yace da hoton da yayi duk wani kokari da zai iya amman ya kasa ko dishe tasirinshi a cikin kanshi.
"To idan wannan skirt din nata ya sake budewa fa?"
Wata murya tayi masa tambayar, sai ga kafafuwanshi na kara sauri, suna takawa zuwa inda ZamZam take tsaye, yanayi yana kallon mutanen da suke ta kai kawo akan titin, kirjinshi har bugawa yakeyi, musamman da yaga ta gyara tsayuwarta, kar skirt din nan ya bude mata...yana karasawa baisan yanda akayi ba, ta bayanta ya tsaya, ko da skirt din zai bude dai zai kareta daga idon mutane
"Skirt din kika kara sakawa? Saboda baki da hankali..."
Taji maganarshi kamar daga sama, a hankali yayi maganar, ta tsorata ne saboda bataji tsayuwar shi a bayanta ba sam, ta kusan minti ashirin akan titin nan tana jiran napep, kafafuwanta har sun fara sagewa. Ta juya, sai kawai wani karamin tsaki ya subuce mata, ba dashi take ba, yaji tsakin, ta ga gilmawar wani yanayi a cikin idanuwanshi da haka kawai yasa ta bude bakinta ta fada masa ba dashi take ba, tsoron da tajine, amman kafin hakan ya faru, taga hannun Faruk daya dago, taji wata kara
"Qwas"
Sai da takai hannuwanta duka biyun ta dafe kanta dasu tukunna kwakwalwarta ta gane abinda ya faru, mamakin da yayi mata dirar mikiya kuma bai hanata jin zafin rankwashin nan ba
Rankwashi fa
Rankwashinta Faruk yayi, a tsakiyar titi, data kalleshi sai taga yasa hannu ya tsayar da wani mai napep daya taho babu kowa a cikinshi, yana mata wani kallo yace
"Ina zakije?"
Kallonshi takeyi da idanuwanta da suka cika da hawaye
"Ina zakije?"
Ya sake maimaitawa cikin wata murya da ta sata furta
"Kofar ruwa..."
Bai jira full address din ba ya nuna mata napep din da hannunshi, sai taga babu musu ta wuce ta shiga, dubu daya ya zaro a aljihunshi ya ba mai napep din yana furta
"Ka kaita har kofar gida"
Ya kuma kara matsowa inda take zaune
"Allaah Yasa mu sake haduwa da wannan skirt din a jikinki"
ZamZam ta kalle shi, kwallin nan da take sakawa ya kara zazzagowa kasan idanuwanta sosai
"Bafa shi bane, ba wancen bane ba"
Ta tsinci kanta da fadi
"Bana gani ai"
Shima yace yana mata wani kallo da ta kasa gane na kashedi ne ko harararta yakeyi
"Bashi bane"
Ta jaddada
"Karya nake..."
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Data bude baki saiya sake mata wannan kallon, sai tayi shiru, tana kallonshi ya dan matsa baya, kamae yana ba mai napep din daya tayar yaja dama. Batasan me take nema ba, kome take so ta sake gani data leka ta cikin napep din da saurinta, yana tsaye har lokacin, kuma wannan kallon ya sake binta dashi, kallon da takeji yana shigarta tare da samun wajajen zama a inda ita kanta bata san dasu ba. Ta sake kai hannu ta shafa inda ya rankwasheta, sai yanzun da babu idanuwanshi akanta ma take ganin karfin halinshi, take kuma tunanin dalilin da yasa ko bata kwada masa mari ba ta balbale shi da masifa.
Wai akan me ma zai rankwasheta? Ita akwai wanda ya taba rankwashinta ma? Sai mutumin da har yanzun ko sunanshi bata ma sani ba
"Lallai..."
Ta fadi wata dariya kasa-kasa na subuce mata, mamaki kawai takeyi, kuma kamar yanda take wannan mamakin haka ma Faruk daya juya ya cigaba da tafiya bayan napep din ta tafi yake wannan mamakin. Shi ba ma'abocin shiga sabgar mutane bane ba, saboda bayason kallo, mutane kuma duk inda zai shiga dole sai sun kalle shi saboda abinda yake fuskarshi, shisa wasu in basu sanshi ba zasuyi tunanin bashi da fara'a, wasu ma kallon miskili sukeyi masa, amman inda zaka ganshi a gida sai kayi zaton wani Faruk dinne ba wanda kagani a waje ba, musamman kaganshi tare da Mama Babba, duk da a gidan nasu ma ba shirgin kowa yake shiga ba.
Tun rannan ZamZam ta makale masa, yana cikin hidimarshi sai yaji tunaninta ya fado masa. Ba zaice a shekarunshi babu macen da ta taba burgeshi ba, akwai tarin 'yan matan da zai gani a hanya, inya kallesu saiya sake kallo, saboda sunyi masa kyau, bai taba budurwa ba, ko irin ta makarantar nan da akeyi, mata da yawa sunsha cewa suna sonshi, ko su aiko a cikin abokanshi a fada masa, sai dai yayi dariya kawai, tunma a lokacin gani yakeyi bata lokaci ne, a yanzun dinma abinda yake gani kenan, to me yasa zai tsaya wata soyayya alhalin yasan ba auren zaiyi yanzun ba? Idan akace ya turo nemanshi za'ayi a rasa.Manya dai yana dasu, amman abinda zai hada manyan dashi inya turasu shine babu.
To ita ZamZam ba zaice kyau tayi masa ba, da waccen ranar, da yau dinma, abubuwan da idanuwanshi suke kallo ba kyanta bane ba, ko daya rufe mata jikinta waccen ranar, babu wani abu daya dinga kallo sai yanda kayan nan suka matseta, sai figigin mayafinta, kallon da tayi masa dama yanayin da yake cikin kallon, yau ma skirt dinta ya fara hangowa, sai yaga bakinta da tayi masa tsaki dashi, daya daga cikin halayenshi, bayason raini, ko alamar raini ma bayaso a nuna masa. Shi wasan nan da akeyi na zage-zage tsakanin abokai ba ayi dashi
"Da kai kazo a babba cikin gidan nan babu wanda zai sha ruwa Faruk..."
Haka Mama Babba kance masa
"Raini ne banaso Mama"
Amsarshi kenan, sai tayi dariya, tunda ko ka girmeshi zaiyi kokarinshi wajen baka girmanka, ana fada dashine saboda suna cewa bashi da kunya, ba kunya bace bashi da ita, raini ne bayaso, yanda ya baka girmanka, to kaima yana tsammanin zaka rike wannan girman karkayi amfani dashi wajen takashi. Shisa baisan sanda ya kai mata rankwashi ba, bashi da saurin hannu, ko kadan bashi da saurin hannu, kafin ya daga hannunshi to yayi masifa tafi a kirga, an karasa kureshi ne. Ita din daice haka kawai yaji yana so ya rankwasheta, ba saboda tsakin da tayi kawai ba, har wannan skirt din da ta saka ta fito dashi.
Cikin abubuwan da yaji yanaso yayi bayan rankwashinta, shine ya saka dan yatsanshi ya goge mata kasan idanuwanta, idonta na haggu yau, da kwallin ya zazzago fiye da dayan, ya goge matashi har sai sun daidaita da dayan idon, sai kuma ace sa ta shiga napep din ya shiga gefe ne sunje har kofar gidansu yaga shigarta gida saiya dawo. Da wadannan tunaninka ya karasa gidan, ya wuce bangaren Ummi, babu kowa a falon, sai kawai ya nufi dakinshi, ya rage kayan jikinshi ya shiga wanka, sanda ya fito an kira sallar magriba, shisa daya sauya kaya saiya sake fita zuwa masallaci. Daya koma kuma saiya wuce bangaren Mama Babba, tun daga falo yake kwala mata kira
"Kai Faruku nafila nakeyi fa"
Ta fadi lokacin data fito da hijabi harda casbaharta a hannu
"Yunwa nakeji..."
Ya fadi yana wucewa hanyar kitchen din
"Hidaya ce tayi girki ko? Dan Allaah Mama kina ganinta tayi mana tuwo?"
Dariya Mama Babba takeyi, daman daya tsaya abinda zata gaya masa kenan, tuwo akayi, amman ya wuce kitchen sai bin bayanshi tayi, yana tsegumi yana bude fridge dinta da na kwance ne, cikin suke ajiye kayan miya da duk wani abu na amfanin kitchen din.
"Miyar tayi dadi, bafa kuka tayi ba, busashiyar kubewa ce"
Faruk ya tsaya da albasar daya ciro yana kallon Mama, sai ta kama yi masa dariya, tunda yama fi tsanar kubewar akan kukar
"Oh nikam zanga yanda zakayi in aka kawo maka tuwo a aljanna"
Wannan karin shine yayi dariyar
"To Mama wanne tsautsayi ne zai fadamun da zan rasa abinda zanci a aljanna sai tuwo? Anan dinma tunda nayi hankali kin kara ganina dashi?"
Ta kama baki
"Mu da muke ci duk kallon mahaukata kakeyi mana ashe...ungo naka Faruku"
Ta karashe maganar tana yi masa dakuwa, shikuwa dariya kawai yakeyi, Maman tana nan tsaye suna taba hira, shine ma yake bata labarin aikin da yaje
"Kinsan Mama wanda fa bashi da kudi bashi dasu, amman babu wani maganar babu kudi a kasa, akwai kudi, suna wajen masu shine kawai..."
Yake fada yana yayyanka kayan miyar daya wanke akan abin yankawa, ko ita Maman batajin zata iya wasa da wuka yanda Faruk yakeyi akan kayan miyar nan, sunata hira ya fito da couscous, tun bai gama hadawa dambun nan ba kamshi ya fara cika kitchen din, saiga Asaad ya shigo da sallamarshi, ya cire suit din jikinshi yana rike da ita a hannu
"Me kake dafa mana Hamma? Kai wallahi na kwaso yunwa..."
Ya karasa cikin kitchen din yana kai hannunshi cikin farantin scrambled eggs din da Faruk ya kwashe, duk kafar da Faruk din ya taka masa saida ya diba yana zubawa a baki...da zafi ma, sai gashi yana fifita bakin, kuma yaki ciro kwan
"Mama sannu da gida"
Asaad ya fadi bakinshi a cike, Mama ta girgiza kai kawai
"Bari in sake kaya in fito.... coke zaka sha ko fanta in fita in siyo mana mai sanyi?"
Cewar Asaad
"Ruwa zansha, kuma akwai a fridge din Mama, abincin nan ban dafa da kai ba Asaad, ban dafa da kowa ba..."
Sai Asaad ya leka fuskarshi
"Haba Hammanmu mijin marainiya"
Saiga Taj ma yana fadin
"A lafiya dai dan Mama, ayi hakuri a gyara mana maganar girkin nan daya cika gida da kamshi, Allaah mana, dan uwanmu mijin marainiya, ko Babbaa"
Ya karasa maganar yana kallon Mama da takeyi musu dariya, haka suke tsokanar Faruk din indai zasu ganshi a kitchen, karfi da yaji sun makala masa mijin marainiya, wai matarshi ta huta, ba akan girki ba, ko yanda yake taya Mama Babba da Ummi da duk wata hidimar gida in dai zaga sunayi, itama tasan Faruk akwai tausayi, Hidaya ma haka tace
"Ai wallahi sai mun zaba mun darje, kai matar Hamma ma sai mun mata screening, dan ba kowa zamu bawa ba..."
Idan taji suna irin wadannan maganganun sai su bata dariya, wani lokacin saita tsokanesu tace
"Itama yarinyar da za'a taimaka a bama dan uwan naku ai mai tsadace"
Sai fa hayaniya ta kaure, ayita kawo mata dalilai kala-kala. Amman kowa a gidan nan da zai bada labarin Faruk ai a bayanta yake, ko Ummi da ta haifi Faruk ba zata gaya mata wanene shi ba, tunda haihuwarshi kawai Ummi tayi, tun yana zanin goyo yake wuni a wajenta, tsakaninshi da Ummi ta shayar dashine ya sake kawo mata, data yayeshi ma kacokan sai ta tattara mata kayan Faruk din, wani abu da har ta koma ga Allaah ba zata daina rokawa Ummi addu'ar Allaah Yayi mata karamci da babban gida a aljanna ba, saboda ta karramata, lokacin da Mummy takeyi mata gorin haihuwa dama mutane da yawa, sai ita ta haifa ta bata riko.
Kuma a zuciyar Mama Babba, Faruku shine danta na farko, shine danta da Ummi ta bata, dan da take so kamar ita ta haifeshi, dan da yake tausayinta, yake sonta, yakeyi mata biyayyar da nata yaranma shi suke kallo suna kamanta mata, tabbas idan matar Faruk ta fahimce shi, zasu zauna lafiya, ta samu mijin da zata zagaya ta nuna ma dangi harma da abokan arziki, sai dai kafin ta fahimce shi kuma fa?
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Faruk na da wani irin baudadden hali da ba kowa yake nunawa ba, halin da Mama Babba ta tabbatar babu wanda zai dinga ganinshi sama da matar da zata rayu a karkashinshi....sai dai kuma ai matar mutum kabarinshi, shikuwa kabari daman ance a wanke yake tas, abinda kaje dashi, shi za'a shimfideka a ciki a mayar da kasa a barku tare...
No comments