Recent Updates

FACALA Page 5

 5

Last free page...

Saida ta sake turara gidan da Sandal flakes din Seemah https://wa.me/2348021689184, dan tana da duka turaren wutar, da aka tashi siya mata package din amarya, babban aka sai mata wato Diamond, to tunda ta turara wannan sandal flakes din Khamis yace duk yafi sonshi sai take ta cancanawa, danma dan kadan inkasa ya biya maka bukata tunda babu ha'inci a wajen hadashi. Data fito sallar Magriba ta sake shiga wanka ta dauro alwalar ishai. 

Shafa wannan, goga wancen, sai gata ana kiran Ishai bata gama ba, a gurguje ta saka wasu riga da wando masu santsi, irin wandon nan ne pallazo, rigar ma free ce da taje har gwiwarta, ta ajiye farar hular da zata saka akan gado. Tun da akayi la'asar Khamis yayi mata text yana fada mata irin yunwar da yakeji, yama kamata ya gama shift dinshi tun wajen hudune, saiya tsaya yiwa abokinshi covering nashi shift din, saboda wani uzuri daya taso masa, ta riga ta gama sake turara abincinta dan bata sakashi a kula ba tasan yanayin aikinsu, tsaf abincin zai iya fita hayyacinshi a kulolin nan bai dawo ba, gara tasan ya kamo hanya tukunna.

Tana raka'ar farko taji an bude kofar falon da bata sakawa mukulli ba, tunda kofar bedroom din nata ma a bude take, duk a zatonta ma Khamis ne, taji takun tafiya har bakin kofar bedroom din, sai kuma muryar mace tana fadin

"Sallah ma takeyi"

Aka kuma sake takawa alamar komawa akeyi, yanda take jiyo zirga-zirgar da akeyi mata, wani zaice ta raba hankalinta biyune, rabi akan sallar da takeyi, sauran rabin akan dudumar da ko suwaye suka shigo sukeyi mata, amman ba haka bane, kai kawo takeji anayi sosai, ga dararraki da maganganu cikin harshen da sai taji kamar tanaso ta gane me ake cewa kamar kuma bata gane ba. Tana idar da sallar kuwa, bata ma tsaya wani azkar ba, da hijabin a jikinta ta fito, cikin madaukakin mamaki take kallon 'yan matan nan.

Dukansu farare ne kal, kusan zatace ma sun fita haske, uku a cikinsu sirara ne kamar ita, sai dayar da tadan fisu jiki. Kuma a tsakaninsu babu wadda ta haura shekara sha tara, daga gani, ita mai dan jikin ma da wahala idan tayi sha biyar. Kamshinsu ya hadu dana turaren wutar da tayi ya cika falon. Daka gansu kaga 'yan gayu da suke cikin gata mai yawan gaske. Ko kayan jikinsu ma zaisa ka sake kallonsu balle kuma kyawawane. Itafa Raihana duk ba wannan bane damuwarta, filet ne a hannun uku daga cikinsu, wannan mai dan jikin cema taga kofi a hannunta data tabbatar kunun ayar da tayi kitimmilin yiwa Khamis ne a ciki

"Anty harkin idar..."

Dayar ta fada, mai gilas makale a idonta, mai bulan frame daya zauna a fuskarta yana kara mata kyau, sai kuma ta kalli daya a ciki tayi mata wani yare da yanzun Raihana ta tabbatar fulatanci ne

"Mun shigo ai munata sallama shiru, sai da Ikhlas taje ta gano mana sallah kikeyi, mu kam har mun wuce kitchen ma, abincin amarya mukazo ci daman"

Ko da Raihana taji ana cewa an daskare, yaune ta gane ma'anar kalmar, sai kuma wani irin bacin rai ya taso mata

"Wanne abincin?"

Ta tsinci kanta da furtawa a hankali, duk da kuwa su duka suka zubo mata idanuwa

"Mun shiga kitchen muka ga abinci a tukunya muka zuzzuba, abincin ma bashi da yawa..."

Daya a cikinsu ta fadi tana samun waje ta zauna akan hannun kujera

"Abinci Dee din ne kuka juyo?"

Raihana ta sake tsintar kanta da tambaya cikin bacin rai da rufewar ido, to su waye su dinma da zasu shigo mata gida harsu wuce mata kitchen saboda zakewa da tsabar rashin hankali?

"Tooo..."

Biyu a cikin suka fada tare suna jan kalmar

"Dee kuma? Waye Dee?"

Dariya taji anyi kasa-kasa, irin ta tsabar rainin nan, inda tana da saurin hannu, tabbas saita karasa ta zabga ma wadda tayi dariyar mari har sai wannan gilashin ya fashe mata a fuska

"Ikon Allaah..."
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Wannan mai dan jikin ta fadi, kafin Raihana ta sake furta wata magana an turo dakin da sallama, ita Khamis ya fara kallo, sai kuma ya kalli 'yan matan, ya fadada murmushinshi har tana hango lotsawar dimple dinshi daga inda take tsaye

"Baffa..."

Biyu suka fada a tare yayin da biyun sukace

"Hamma"

Su duka da murmushin jin dadi a muryoyinsu

"Kuce manyan bakine a gidan namu, 'yan matan Mummy, yaushe kuka dawo?"

Cewar Khamis a madadin amsa gaisuwar da suketa jera masa, lokacin ya karaso cikin falon, ya samu kujera ya zauna da alamar gajiya sosai a tare dashi, ya dan sake kallon Raihana da take tsaye yana fadin

"Madam...sannu da gida"

Sai kawai taji ranta ma yana neman ya sake baci

"Dan Allaah a zubomun abinci sai ki dawo kiji da bakin naki, nikam da yunwa na shigo"

Kafin ma ta bashi amsa 'yan matan nan sun dauke masa hankali daga kanta suna bashi labari cikin yaren da ba fahimta takeyi ba. Saita juya ta nufi hanyar kitchen, dan ta samu zuciyarta ta danyi mata sanyi, saita tarar da wani bacin ran a kitchen, sun fito mata da kayayyaki, filet wajen guda nawa, ga kwalin wasu kofuna da suka fito dashi aka yaga kwalin, ita da ta kammala komai, abincin ma wajen zubawa duk an zubar har a kasa, sai kace wasu kananun yara. Ga Jug din kunun ayar data mayar fridge dan ya kara sanyi nan a bude, abinda ya rage a ciki bai kai kwatar karamin kofi ba. Ta sha yiwa ZamZam dariya akan saurin kukanta, sai gata yau hawayen bakin ciki na neman balle mata.

Tukunyar abincin nan babu komai a cikinta sai barbadin shinkafa, ga kular data zuba sauce nan ma an kwashe tas, ta kusan mintina goma a cikin kitchen din nan numfashi kawai take ja tana saukewa cikin tsananin bacin rai, sai ga Khamis ya shigo

"Ray Babe"

Ya fadi yana wani zakaka murya, ta kalle shi kawai

"A bani abinci dan Allaah"

Muryarta can kasan makoshi tace

"Sun kwashe duka, ina sallah suka shigo, kafin in fito sun kwashe duka"

Sai kawai yayi murmushi

"Allaah Ya shirya, wannan yaran da ci...da basu samu abincin bama ai da mun shiga uku da tsegumi, inajin har Mummy sai ta tayasu...zo muje kawai..."

Ya kama hannunta yana fara janta su fita daga kitchen din zuwa falo yana cigaba da fadin

"Bari a karbomun a wajen Mummy..."

Lokacin da suka karasa falon kuwa ga mamakin Raihana sai cewa yayi

"Jawda karbo mun abinci wajen Mummy tunda kun cinye wanda aka dafamun"

Sai taga daya a cikinsu ta mike tana dariya, filet din hannunta ta dire akan kujerar data tashi tana ficewa, ya samu waje ya zauna, hakan ya tilastama Raihana zama itama

"Kofa gaisawa ba muyi ba ka shigo"

Cewar mai gilashin nan, suka gaishe da Raihana data amsa fuskarta babu ko digon fara'a

"Ray, kinga Jawda data fita, ga Ikhlas kanwarta, sune yaran Adda Badr da nake fada miki"

Bata manta ba, Adda Badr itace babbar yayarsu Khamis, a yanda yake bata labari, lokacin da akayi mata aure tana da shekaru goma sha shida ne, dan a dakin mijin ta karasa sakandiri dinta, ya kuma sakata a jami'a, sojane da ya rasu akan aikinshi, yaransu biyu duka mata, sanannen family ne tayi auren, tasha wahala ma a hannun dangin mijin da suka dinga ganin kamar bata dace da dan uwansu ba, kowa yayi mamaki da suka bar mata rikon yaran bayan rasuwarshi, ko dan ance mutuwarce ta dake su matuka, kuma kafin ya rasu yanata jaddadawa mahaifinshi da yake tare dashi a asibiti da a kula masa da iyalanshi da farin cikinsu, kar a bar yaranshi suyi kukan rashinshi.

Sai dai su kansu su Khamis din sunsan inda Addan ta sake aure, tabbas da tuni sun karbe su Jawda, duk hutu suke tafiya Abuja wajen dangin mahaifin nasu, ko yanzun dinma washegarin daurin aurenshi da suka zo, suka juya dasu Ikhlas din, sai yau suka dawo, a cikin yaran babu wanda baije aikin Hajj ba, Umra kuwa Khamis ba zaice ga adadin da sukaje ba.

"Ga Alina, ga kuma Huda, yaran Baffa Chubado ne, kanin Mummy, kusan rabin rayuwarsu dai anan suke yinta tare da Mummy..."

Alina ta karbe zancen da fadin

"Ai mu gidan nan ma zamu dawo da zama Hamma..."

Raihana ta kalleta cike da faduwar gaba

"Nan ina? Lallai yara, yanzun ma zaku zo ku koma ne ai, babu wanda zaizo ya damarmun mata"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Sai sukayi dariya, Huda na cewa

"Lallai Hamma, shisa fa mukaso ka kawo mana tamu dan muyi yanda muke so a gidan nan, kana gani abinci muka wuce kitchen muka diba, Anty tace na Dee ne..."

Ita Raihana ta rasa abinda takeji koya kamata taji, idan ma akwai magana a bakinta to ya rufe ruf, ikon Allaah kawai take kallo 

"Wannan dinma taku ce tunda ni na kawota, right Babe?"

Yayi maganar yana kallon Raihana, tare da riko hannunta, sai kawai tayi masa wani murmushi, ya numfasa da nufin yin magana sai ga Jawda ta dawo da kuloli har guda biyu a hannunta

"Naga anyi masa fa Baffa, shine na dibo maka ita"

Da dayan hannunshi yayi mata alamar jinjina, data ajiye kulolin sai ta wuce kanta tsaye kitchen din Raihana ta dauko filet harda karamin bowl ta fara zuba masa abincin

"Banma san ko Anty zataci ba, nikam ban dibo da ita ba"

Sai lokacin Raihana tace

"Na koshi"

A takaice, Jawda ta dan tabe baki, ta gama zubawa ta mikawa Khamis daya saki hannun Raihana ya karba, sai ma ya zame ya sauka kan kafet din, Jawdan ya sake sakawa ta samo masa waje da ruwa ya wanke hannunshi

"Ki dauko mun fanta a fridge din nan idan akwai saura, in babu kowanne lemo ma zaiyi..."

Ta dauko masa, suma ta jido musu suka dawo suna tisa hira a falon, kuma in ba don Khamis da yakan juyo ya danyi kokarin sakata a hirar da rabinta fulatanci ne, sai Hausa da wani turanci da yasa Raihana ta raina NCE din da take balain ji dashi, dan sai baza kunnuwa takeyi, amman yaran nan turanci sukeyi kamar zasu tauna harsunansu.

Lallai akwai babbar damuwa!

Ta raya a cikin ranta, sai taji kamar yar siririyar iskar da ta kada a cikin dakin ta kwaso mata wata murya data rada mata

Kiyi fatan iya wannan ce damuwarki Raihana...

Ta kalli Khamis da yake dariya sosai, da alama wani abinne suke fada da bata gane ba shisa bai bata dariya ba, sai kawai ta tuna ranar farko daya kirata a waya

"Ina magana ne da Kawarmu ni da ZamZam?"

Batasan ko ta gane muryarshi bane saboda a tsakanin ranar daya karbi lambar zuwa washegari ta duba lafiyar sifikar wayar yafi sau saba'in, haka ta dinga bi tana dubawa wai ko dai ya kira bataji ba, ko kuma dan tasan bata jiran kowanne kirane sai nashi, dazun da ZamZam ta shigo gidan kuwa har saida ta zageta akan yanda take ta duba waya

"Wai uw*r meye a wayar da naketa miki magana bakya jina? Kinsan dai na tsani ina magana ayi banza a kyaleni"

Saita kalli ZamZam, kallo a karo na barkatai, tanaso ta gane dalilin da yasa bata kwaso mata maganar Khamis ba, ko ta manta sun hadu da wani ne?

"Kana magana da Raihana ne, Kawar ZamZam, kai kam meye hadina da kai?"

Sai yayi dariya, irin dariyar nan da yakeyi yanzun, kamar babu wani abu da yafi abinda ta fada nishadi, ko da yake ai daga lokacin zuwa yanzun tasan Khamis bashi da matsalar dariya, kullum cikin fara'a yake, ko idanuwanshi ka kalla sai kaga kamar yanayi maka dariya, akwai wani yanayi a fuskarshi da zaisa kaji zaka iya magana dashi batare da fargabar zaiyi maka wulakanci ba. Ba tasan ya zata misalta abin ba, amman dai bangaren daya zaba yake koyon horarwa akai yanzun haka a aikin likitanci, bangaren yara, ya dace dashi matuka. Saboda yayi kama da irin mutanen da zaka aminta ka basu rikon yaranka a haduwarka ta farko dashi.

Suna nan zaunen kuma sai sukaji sallama, Raihana ta amsa a hankali, tunda su Khamis suma duk sun amsa sallamar

"Adda..."

Cewar Khamis, Badriyya ce, Raihana ta ganeta, da suka shiga bangaren Mummy gaisheta ita da Khamis din taga Addan itama

"Wato zuwa kukayi kuka mike kafa, kuka barmu shiru ko? Yayi muku kyau"

Adda Badr ta karashe tana amsa gaisuwar da Raihana takeyi mata

"Amarya karkice bamu lekoki bafa, bari mukayi ki warware gajiya, sai kin ganmu har kingaji"

Idan ka kalli Adda Badr, saika rantse ka sake bata haifi su Ikhlas ba, gata kamarsu, tasha gayu abinta, mayafinta ma a kafada ta yafoshi.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Raihana tanata wani sauke kai, saboda taji 'yar kunyar Addar a matsayinta na Babbar yayar mijinta, ga Khamis da zuwa lokacin ya gama cinye wainar shi, harya wanke hannu, ya jingina bayanshi ne a jikin kujerar da take zaune har bayan nashi na taba kafarta guda daya, sannan kanta babu ko hula. Ta dauka Adda zata tattara kansu Ikhlas ne su tafi, sai taga ta samu waje ta zauna itama sun dasa sabuwar hira.

Tun Raihana na gyara zama tana duba agogo, goma tayi, sha daya ma tayi suna nan zaune suna wannan hirar, ita kuwa kanta har ya fara ciwo saboda baccin da takeji, tana samu ta dan rama wanda Khamis ya hana matane da safe, to yau batayi baccin ba tunda tanata zumudin zuwan ZamZam, ta hango yanda zatayi baccinta a tsanake a jikinshi idan suka gama cin abinci, to ga wannan lamarin hirar dasu Adda suka dasa da ta tabbatar da yafi zare tsayi lokacin da sukaji sallamar Mummy ta bankado dakin nan ta shigo, yanda karar takunta yake amsawa

Shirim, shirim...

Saika rantse da Allaah wata sangemiyar mace zaka gani irin mai kibar nan bawai doguwar bafullatana da jikinta yake a murje irin Mummy ba, tsabar yanda Raihana taji ta kidime sai da ta kusan zamowa ta tiko daga kan kujerar da take, shi kanshi Khamis din da saurin gaske ya janye jikinshi daga nata, Mummy ta hadasu tana watsa musu wani irin kallo, ko gaisuwar da Raihana tayi mata cikin rawar murya bata amsa ba, hargowa takeyi tana karawa cikin harshen fulatanci kamar zata kai duka, duk sukayi tsit, kafin daya baya daya su mike suna fara yi musu sallama, ita kuma Mummyn saita sake yiwa Khamis din yare kafin ta rufa musu baya, Raihana tabi bayanta da kallo, ita lace din Mummy ne ma ya dauke mata komai yana maye mata gurbinshi da mamaki.

So take ta tuna inda ta taba ganin irinshi, dan tabbas shekarun da aka buga wannan leshin suna da yawan gaske, yellow ne kuma irin mai dadin kwatancen nan, wani kalar abune akayi masa ado dashi kamar kananun mudubi, kamar dai an watsawa Mummyn fasashen mudubi a jiki, shisa ashe take ta walainiya, in badai bata gani dai-dai ba, wata koriyar sarkar murjani ce a wuyan Mummy kwankwareriya, kuma kamar da jambaki shima kore. Ko dai bata gani dai-dai ba?

Dariyar da Khamis yayi a hankali ta kurda cikin tunaninta

"Yau kinga fadan Hajiya Mummy ko?"

Ta rasa abin fada, sai tayi masa murmushi da hakoranta

"Fada fa take tayi an barta ita kadai kamar mayya, akan me ba zan daukeki mu tafi can bangaren ayi hirar gabaki daya ba...kinsan ita bata da matsala, kawai dai bataso taga munayin nisa da itane ko kadan, bana gaya miki Adda kadai ce aka kaita Abuja ba?....mu daije mu kwanta dan zan fita da wuri...a hankali zaki saba da kowa da halinshi..."

Ta kalle shi, baccin da takeji ma ta neme shi ta rasa 

"Ki tashi muje..."

Yayi maganar yana mikewa tare da kamota ya dagota zuwa jikinshi, ya sumbaci wani waje a tsakanin girarta a hankali yana saka idanuwanshi cikin nata sosai

"Mu kwanta?"

Yayi tambayar da ta share wani fili cikin kan Raihana tana kasuwa da ma'anonin da take dauke dashi

Sai kawai ta ture su Adda tana rungumar mijinta.
Sai dai akwai yanda zata rungumi Khamis batare da ahalinshi sun jingina dashi nauyinsu na danne ta ba?


[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: 

No comments