FACALA Page 4
4
Dakinta take karewa kallo, fentin dakin take kallo, ruwan toka ne da shekaru suka sauyawa kamanni, dan har wani fari-fari yakeyi ta wasu bangwayen, dakin karamine, danko katifarta karamace, irin ta yan makaranta, sai sif din kayanta da tama yi mata kadan, dan akwai akwatuna harda jaka da suke can saman sif din, ta kuma buga abin rataye kaya a jikin bango daya na dakin, nan take rataye jakunkunanta da wasu cikin kayanta ma. Daga kusurwar dakin, ta gefen sip din, akwai dan karamin teburi irin na robar nan hade da kujerarshi, a kasan teburin nema zaka hangi tarin takalmanta data jerasu. Yanda duk zatayi manejin space din dakin karya kara cushe mata tana wannan kokarin. Dan filin daya rage inta shimfida dardumar sallah babu wajen da zaka samu kuma.
Ta tsayar da idanuwanta akan rigar nan, rigarshi ruwan kasa ce mai duhu sosai, kuma itama dai turtleneck dince, jiya haka ta dauko rigar ta ajiye akan katifarta tanata kallonta kamar in ta tattara hankalinta akai rigar zatayi magana ta amsa mata tambayoyin da suketa shawagi a cikin kanta. Data kai rigar hancinta ta shinshina sai taji dariya na neman kubce mata, kuma ta sake shinshinawa ne saboda bataji alamar kamshin turare a jiki ba, abinda hancinta ya jiye mata ba wari bane ba, rigar wani abu takeyi, wani abu 'Manly' da bata taba sanin akwaishi ba, tunda ita yanda take kallon maza, in dai baka kamshin turare, to kana tsami, ko na rana, zufa ko ma dauda
"Ke kika daukarmun kwai a kitchen?"
Maganar Ubaida da take a kufule ta kutsa mata cikin kai, dai-dai lokacin da taji shigowar wani kuda a sukwane kamar yana jiran a daga labulen dakin ne ya samu hanya yana kuma gayyato mata 'yan uwanshi da suka rufo masa baya, ta kalli yanda Ubaidar ta hanqare labulen tana hadeshi ma da jikin bango ta dafe
"Ki sakarmun labule Ubaida, kinsan kudaje zasu shigomun kuma banaso..."
ZamZam ta fadi a hankali saboda yau ita bata neman tashin hankali da kowa
"Ina tambayarki kwaina da kika dauka kina mun maganar wani banzan kuda"
Gyara kwanciyarta ZamZam ta sakeyi
"Ina kwaina Malama?"
Cewar Ubaida
"Saiki hadu dake da wanda yace miki nice na dauka kuzo ku matseni in fito dashi ai"
Ai kamar ta watsawa Ubaida ruwan zafi, sai ta fara daga murya
"Karfa kiga ana miki shiru, babu wanda yake tsoronki a cikin gidan nan, Nasiba tace mun ke kika shiga kitchen din"
Ta shiga kitchen dazun tabbas, ruwan lipton ta dafa ta dawo saboda mararta da taji tana karta mata, tana tsaye a kitchen din ya tafasa ta samu kofi ta juye ta fito, tsaki taja tana juya kwanciyarta. Har Ubaida ta karaci surutunta ta saki labulen bata tanka mata ba, duk da taji zafin
"Katuwar asarar"
Data kirata dashi, amman haka ta danne ta kyaleta, tunda dai daga ita har Nasibar babu wanda zata daku a hannunshi, sun gwada, haryi mata taron dangi sun gwada, ta hadasu tayi musu lilis, shari'a har gaban Baba Alhaji, Ubaida na fada masa hakorinta girgidi yakeyi inda ZamZam ta gabza mata naushi. Babu wanda yaji dadin yanda Baba Alhaji ya hadasu yayi musu fada su duka. Amman tun lokacin babu wadda ta sake gangancin tararta da dambe, sai dai cacar bakin da yau ko karfin biye musu bata dashi.
Karar da wayarta tayine yasa ta tashi ta cirota daga cajin data saka, ta riga tasan Raihana ce, da murmushi ta daga kiran hadi da kara wayar a kunne tana fadin
"Ray-Ray amaryar likita, ai ban dauka zaki tuna dani a kwana biyu kacal ba, ke da akasa a daki anata miki alluran soyayya"
Dariya Raihanan tayi daga dayan bangaren
"Kina da maganar banza wallahi...ai da fushi nayi sai na tuna baki da kan gado, ba lallai ma kigane na zuciya ba, gara in kira in fada miki sai in kara tafiya wanu fushin"
Wannan karin ZamZam ce tayi dariya
"Me nayi ni Fadimatu?"
Duk da bata ganin Raihanan tasan harararta takeyi
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: "Wai kawai sai in nemeki in rasa ZamZam, ko kowa zai gantalar dani ai ban dauka kina ciki ba, kuma na dinga kiranki wayarki a kashe, kinsan yanda na shaka? Sai su Shamsiyya fa, su hudu aka barmun, suka dinga wani bare-bare da Dee yazo da abokanshi, shi da kanshi saida yace kina ina bayan sun tafi, nace zazzabine ya kamaki..."
ZamZam ta katseta
"Ciwo kika doramun?"
Sai sukayi dariya a tare
"To uw*rme kike so ince?"
ZamZam na dariya ta amsa da
"Ke wannan Amma Hasee dince fa tana ganina tace in tafi gida wai ba za'ayi wani siyan baki ba, suma gidan zasu kara gyara miki su tafi, naga tayi bake-bake ne, nasan ba zata barni in shigo muyi magana ba, bana son damuwa kinsani, ga wayata ashe ma mutuwa tayi tana cikin jaka ban kula ba sai bayan na dawo gida"
Salati Raihana ta ja tana direwa
"Amma nada matsala wallahi, dan Allaah kiyi hakuri, duk da naji haushi saida nayi tunanin dole akwai dalilin da yasaki tafiya, to da baki kirani bane na kara kulewa fa"
ZamZam ta girgiza kai
"Ina zan kiraki ke da kike kan tsuntsun soyayya? Ke banza kinsan meya faru? Fita nayi kallon kida kofar gidan surukanki fa, zip dina ya bude, gashi kinsan wannan skirt dinne daya mugun matseni, dagani sai pant..."
Dariyar da Raihana ta kwashe da ita harda tari yasa ZamZam din watsa mata zagi, amman ta kasa tsaida dariyarta
"Inalillahi, wai zuwa kikayi kikai musu free show kawata?"
Dariyar da Raihana takeyi da kuma yanda tayi maganar sai yasa ZamZam murmusawa itama
"Bansani ba, aina fasa baki labarin tunda wulakanci zakiyi mun..."
Hira suka dan taba bayan Raihana ta gaji da jera mata magiya akan ta fada mata ya aka kare amman tace ta fasa, kafin suyi sallama ne take tambayar ZamZam din yaushe zataje
"Ke bafa yanzun ba, kibari mijinki ya gama hutunshi ya koma wajen aiki sai in shigo..."
Akan hakan sukayi sallama. Kuma duk nacin kira kan kira da Raihana takeyi mata akan ta taimaka taje, fur takiya. To kawai sai taje suna hada idanuwa da Khamis? Me ma zataje yiwa Raihanan ko sati daya aurenta bai rufa ba? Tayi fushi ta huce yafi a kirga. ZamZam bata shirya zuwa gidan ba sai da ta cika satika uku cur, a wadannan satikan, na farko ne kawai ta dauka Faruk na fado mata, rigar tashi ma da take rataye, da zatayi wanki ta hada ta wanke da ita, ta kuma ninke ta saka can kasan kaya. Ita da take da abubuwa da yawa, ina zata tsaya wani tunani da ba zai amfaneta ba?
Ko ranar litinin din data gama shiryawa, Hajiyayye kawai ta samu a daki take ce mata zata fita tana dorawa da
"Gidan Raihana zanje ko da kinga nayi yamma sosai ban dawo ba"
Sai Hajiyayyen ta kureta da idanuwa
"Amman kinsan yanzun ba kamar da bane ko ZamZam? Ba zai yiwu ki dinga sintirin zuwa mata gida ba ko da yaushe, kema ki nutsu ki fitar da miji kiyi aurenki"
Tasan babu wanda ya damu da lamurranta a fadin gidan nan, a ciki kuwa harda Baba Alhaji, Hajiyayyen ce ma takan nuna kamar ta damu wani lokacin, tunda in ta fita tayi yamma takance
"Kin dade fa, ki daina bari yamma nayi miki a waje haka"
Amman sau nawa zata zari mayafinta ta fice batare da kowa ya damu ba, ta kuma dawo babu wanda zai tambayeta daga ina take, yau daya kamata ace wannan 'yar kulawar data samu taji dadinta, sai ta bata mata rai. Gidan Raihana fa tace zataje, ko dai Hajiyayyen bataji da kyau bane ba? Ta kasa cewa komai, harta fice maganganun dawo mata sukeyi, ta nutsu ta fitar da miji? Wacce irin nutsuwa? Sai kawai ta sauke numfashi tana samun napep ta shiga, saima da suka kama hanya tukunna ta tambaye shi ko nawa zata bashi. Yanda Raihanan ta buga tsalle tana rukunkumeta kamar sunyi shekaru basu hadu ba ya wanke mata takaicin data fito dashi
"Kai jama'a, kinji yanda nakeji kamar an daddaureni...wai yau nice nayi sati uku ban fita ko ina ba"
Cewar Raihana, ZamZam tayi dariya, ta samu kujera ta zauna
"Daureki akayi mana yarinya, da igiyoyi har uku, kuma wannan qullin In Shaa Allaah har aljanna, ya dauru tamau, saiki kara gyara zama"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Murmushinta Raihana ta fadada sosai, har wani dan numfashi ta sauke, ai Khamis mijin da zataso ta kasance dashine daga nan har aljannar. A sati ukun nan ya bude mata ido da wata irin soyayyarshi mai sanyi
"Wai ko ruwa ba zaki kawomun ba...haka zaki sakani a gaba kina kallo?"
ZamZam tayi maganar tana harararta
"Ruwa? Ni zan kawo miki ruwa dan kinzo gidana, lallai baki shirya shan ruwa ba, tashi fa zakiyi mu shiga kitchen tare, dan wallahi babu abinda na dora tunda Dee ya fita, shi daman baya karyawa da wuri, to haka yake fita sai yaje can yake karyawa, nikuma shayi kawai nasha da kwai, cikina harya fara kullewa"
ZamZam ta bude baki tana kallonta
"Kitchen? Wai ko dai soyayyarce ta rufe miki ido har bakya gani sosai, ni idan ma munje kitchen din me zan iya tsinana miki?"
Sai Raihana tayi wata dariya
"Ai ko ruwan zafi kin tayani dorawa, ki gyaramun kayan miya kuma...nifa wallahi Zam ba abinda nake so ingani sai mijin da zai kwasheki..."
Yanda ta karshe maganar da wata dariya kasa-kasa yasa ZamZam kallonta sosai
"Bangane mijin da zai kwasheni ba?"
Saboda akwai wani yanayi a muryar Raihanan da tayi maganar dashi wanda bai zauna mata ba
"To kwasa mana ZamZam, dan girkin nan ma da akace adon kowacce mace ne, idan maki za'a bayar cikin dari ba zaki tsira da goma ba"
Wani abu ya taso yayi tsaye a kirjin ZamZam, magana Raihana takeyi kamar batasan komai ba, kamar batasan dalilin ba
"Dagewa zakiyi ki dinga zuwa gidan nan munayin abubuwa fa, dan wallahi akan abinci maza ba kirkine dasu ba, shi kadai saiya girgide miki aurenki..."
Kallonta dai ZamZam takeyi har lokacin
"Ba kallona zaki tsaya kinayi ba, wani zaki lallabo ki samu ya turo, mu ma ta nan asan yanda za'ayi asiri ya rufu, ko yar jalof din nan ce, shinkafa da miya dai da an samu dan salad ko batayi dadi ba sai kiga an tura cikin dadin rai, ni addu'a nake ki samu dan gargajiya wanda bai damu da yawan girke-girke ba, ko garau-garau kika wargatsa muku sai kiga kunci kayarku, ba irinsu Dee ba"
Idanuwan ZamZam na kanta, ta sauke numfashi, ba yau Raihana ta fara mata magana akan girki ba, amman na yau dinne takejin shi daban, inda batasan wacece ita ba sai tace ko goranta mata abin takeyi, amman Raihana ce, idan taji wani zai goranta mata, tana sahun farko a cikin masu kareta, ko ma tace ita kadaice take da yakinin zata kare mata fada
"To ki sake addu'ar nan dan Allaah Ray, in samu mai kudi, gidan da sai dai a girka a kawomun ina zaune, in cinye a kuma daukemun kwanon"
Sai Raihana ta saka dariya, dariya ta gaske
"Lallai baki da hankali, to ke a ina zaki samo mai kudi haka?"
Itama kuma ZamZam din sai tayi dariyar
"Ai Allaah nace ki tayani roko, babu kuma abinda yafi karfinShi"
Dariyar Raihana ta sakeyi harda girgiza kai
"Ni dai ki tashi muje matar mai kudi"
ZamZam na mikewa take fadin
"Allaah Ya amsa bakinki. Amin"
A gabanta Raihana ta fito da kaza, a yayyanke take an saka a cikin irin ledojin Ziploc din nan, ta fito mata da cefanen ta gyara mata tattasan, da tomato tana wanke mata komai
"Ga albasarki, kinsan na tsani yanka albasa..."
Duk omon da zata saka ta wanke hannunta sai ta wuni tanajin warin a hannunta.
"Practical zaki fara tun yanzun, idan kikaje gidanki kin huta"
ZamZam ta harareta
"Sai dai uw"r practical"
Raihana na danne dariyarta tace
"Haba kawata, dan Allaah ki taimaka, ina da morning fresh saiki wanke hannunki dashi"
Duk da haka saida Raihana ta samu leda ta saka hannunta a ciki, dan ma taga Raihanan na yayyanka wannan naman kazan kananu ne, kuma aikin kamar ba dan karami bane, tunda kazarce guda daya sukutum, idan itace ma saita shafe awanni tana abu daya. Kuma sunata hira, Raihana ta soya wancen ta kwashe, ta zuba wancen, ta barbada wancen, cikin kasa da mintina arbain saiga kamshi yanata tashi. Hirar da suke bai hana ZamZam saka idanuwa sosai akan abinda Raihanan take ba, so take ace ta haddace komai.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Ta gama hadaddiyar jalof dinta, wannan kazar wata sauce ce taga tayi, kayan miyar yin sauce din yayyankasu tayi da kanta, wani tattasaine, kore, da ja da kuma yellow ta hada waje daya, albasar kanta wani manyan yankane taga Raihanan tayi, lokacin da suka gama da kitchen din, ZamZam tayi mata wanke-wanken kayan da suka bata, ita kuma Raihana ta zuba musu abincin a babban tray, ta saka musu sauce din a gefe, ga kuma madarar strawberry ta kamfanin hollandia, mai sanyin gaske da ta dauko mata tana cewa
"Ga mutuniyar, jiya nace Dee ya siyo zakizo tunda kinaso, duka katan din ya kawo. In zaki tafi saiki kwashe tunda ni kinsan ba sha nakeyi ba"
Asalima duk wani abu daya danganci madara Raihana bata sha, ba don bataso ba, bata mata ciki yakeyi, saita wuni tana gudawa da ciwon ciki, shisa ta hakura. ZamZam saita kasa bude bakinta tace komai, ita kuka baya mata wahala, abin farin ciki da akasin hakan yanzun sai hawaye ya balle mata, ganin yanda tayi shiru yasa Raihana yin dariya
"Kuka zakiyi wai? Kefa banzace"
Taso tayi dariya itama, amman ta kasa, tanaso a sota, tana so a nuna mata kulawa, a duniya idan rashin kulawa kan zama ciwo, to tasan yawo kawai takeyi ana ganinta, amman ya gama bin duk wani lungu da sako na jikinta ya kassarata
"Nagode Ray, Allaah Ya kula dake da lamarinki"
Ta amsa da
"Amin 'yar kanwata"
Tsaki ZamZam taja, Raihana tayi dariya, daman abinda ta tsammata kenan, wata biyu da yan kwanaki ta bama Raihanan, amman tana son tsokanarta dashi wasu lokuttan. Da ZamZam takai lomar farko bakinta, sai taji kowanne dandano yayi ma harshenta wata kyakkyawar runguma, abincin yayi dadin data kwana biyu bata dandana irinshi ba, ta dan dago ta kalli Raihana da take cin abincin tana dan danna wayarta. Sai ta sauke numfashi, ta cigaba da cin abincin, a hankali kuma take karewa falon kallo, tasan kayan dakin, har yanda suke bayan an jerasu saida tagani, tunda Khamis ya dauka a hoto ya turawa Raihana, ita kuma ta nuna mata.
Amman yau sai taga ya kara kyau, komai ya zauna a muhallinshi, ga frames din da suka kara kawata falon, ga wani sanyayyen kamshin turaren wuta da tunda ta shigo takejin shi daman, bata ga laifin Raihana data dinka kururuta turarukan Seema ba, https://wa.me/2348021689184, tace zata sammata kabbasa spray din
"Ina ma kabbasa spray dina?"
Raihana ta hadiye abincin da yake bakinta, ta kurbi ruwan da yake ajiye a cikin roba sannan ta amsa
"Komai na nan na hada miki, in kika tashi tafiya dauka kawai zakiyi"
ZamZam ta jinjina kanta tana cigaba da cin abincinta, a gefe daya kuma tana kara taya Raihana murna, dan yau kam kome tayi sai taji ta burgeta, ga gidanta ita kadai, ta wataya yanda take so, ga kuma miji na nunawa a dangi, sannan ga girki ta iya. Ko da tazo yima kanta addu'a, sai taji dariyar Raihana ta dazun ta dawo mata
Anya zata samu rayuwa irin wannan kuwa?
To idan ta samu ma ta dace da ita ne?
Duk da ance rai da buri...!
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: LubnaSufyan ?
#WomenOfWords
#09035723778 (Whatsapp number)
Littafin nan na kudine da za'a iya samunshi a manhajar Arewapen a yanzun, bayan mun kammala shafuka biyar na dandano. Zai kuma fara sauka a manhajar telegram 15 ga watan nan da muke ciki In Shaa Allaah.
To Aisha Abdu Gusau, with Love.
No comments