FACALA Page 3
3
Tunda ta shiga takai akwatin nan, ta tabbatar da ta mikawa kanwar mahaifiyar Raihana, ta fito ta dawo kofar gidan da akace nan ne na surukan Raihanan. Dan tunda zasu wuce taji alamar kida hankalinta yayo nan. Ance ba'a so mutane da yawa suzo, amman da alama wasu adaidaita sahu suka hau suka biyo bayansu, ko fitowarta falon Raihanan a cike yake dankam, mata sunkai su 20, harda kananan yara, in ba kuma dangin Khamis din bane ba, koma menene a halin yanzun ba damuwar ZamZam bane ba, ita da take tsaye tana kallon ikon Allaah, mazane danqam, da shigar farauta a jikinsu, irin kayan sakin nan da zakaga yawancin mafarauta dama yan daba suna sakawa. Daga inda take tsaye ma sunfi su 40. Sai masu kidan da suka zagaye
"Wai sai da Taj yazo da masu kidan gangin nan dai?"
Taji wani matashi da yazo wucewa yana fadi cikin zallar takaici, ta tsinci kanta da murmusawa, sunan daya kira na saka abubuwa da yawa dawo mata. To ko dai kafiya da gaddama a jinin masu sunan take? Itama tasan Tajuddeen guda daya da zai iya aikata abinda mutane hamsin zasu taru suna ce masa kar yayi. Tuntube ta kusanyi saboda bata kallon gabanta, wata 'yar tsakuwa ce ta shige mata ta gefen takalmin, dan taji ta takata bayan ta gyara tsayuwarta tana kokarin karasawa wajen taron mazan nan, saita dan zame takalminta da nufin fitar da tsakuwar, ba zatace ga asalin abinda ya faru ba, tasan dai ta dan rankwafa kadan, ta kuma ji karar budewar da zip dinta yayi, taji iskar da ta kada wani abu har cikin tsokar cinyoyinta
"Inalillahi wa ina ilaihi raji'un..."
ZamZam ta furta tana runtse idanuwanta, tunda taga zip din nan ta tsakiya zuciyarta bata aminta ba, ita duk wani dinki idan ba Deeni bane yayi mata shi ba gamsar da ita yakeyi ba, tafi jin ya zauna mata a dai-dai. Sai dai sauran kwana goma bikin Raihana, tana zaune a falon Hajiyayye tana yanke farcenta sai ga Yayansu Imam ya shigo dakin da sallamarshi, sai data bari sun gama gaisawa da Hajiyayyen tukunna ta gaishe dashi a takaice, da yace
"Ashe biki zakuyi..."
Saida ya kara da kiran sunanta tukunna tasan da ita yake, cike da mamaki ta daga masa kai
"Ma Shaa Allaah, Allaah Yasa alkhairi, Allaah Ya kawo miki miji nagari kema"
Wani abu ya taso tun daga yatsan kafarta da take rike dashi ta kasa cigaba da yankan farcen ma har cikin kanta, yana toshe mata makoshi
"Ankon fa? Ko ba zakuyi ba?"
Gyaran murya ta danyi, duk da haka muryarta a shake ta fito lokacin da tace
"Nayi, Yayaa Aryan ne ya bamu kudi ni da Raihana, sai na siya a ciki"
Ya jinjina kanshi
"Angode masa...idan irin wannan abin ya taso ki dinga magana tunda wuri sai ayi miki a gida, kinji ko?"
Kai kawai ta daga, haka kawai hawaye yake neman balle mata
"Kije gidan Adda Habiba zata aunaki, zan aika mata da kaya sai ta dinka miki, ki kara kiyi fitar bikin, ungo wannan ko zaki kara siyan wani abin"
Tasa hannu ta karba, ko godiya saita kasa yi masa, har yayiwa Hajiyayye sallama ya fita
"Haba ZamZam ko godiya fa banji kin yiwa Yayan naki ba"
Sai tasa hannu ta share hawayen da suka zubo mata, to ta ina zata fara? Abinne duk takejin shi wani iri, yaushe suka fara damuwa da lamarinta? Kudin ta kara dumtsewa, sai bayan ta shiga dakinta ne ta kirga, dubu biyar ne, ta dauko wani littafi ta bude tsakiyar shi ta saka kudin nan. Daga ranar daya bata su zuwa yau kuwa babu kalar talaucin da bata shiga ba, amman ta kasa kashe ko Naira biyar a cikin kudin nan, kullum saita bude ta shafasu ta sake mayarwa. Ba tama je gidan Adda Habiban ba, itace tazo gidan da daddare, wai sunje barkane matar abokin mijinta ta haihu, shine suka biyo gidan ita da mijin, saita dauki rigarta da skirt ta bata kawai tace daidai girman zatayi mata.
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Da aka kawo kayan, dinkin yayi kyau, tunda Adda Habiban kwararriya ce, sannan tsohon hannu, takai shekaru goma sha tana wannan sana'ar dinkin, tun tana budurwa har yanzun da take da nata iyalin. Kayan kala biyune, atamfa sai kuma wani leshi da laushinshi kawai zai fada maka mai tsada ne.
Dinkunan sunyi kyau sosai, matsalar kawai ba Deeni bane ya dinka mata, inda Deeni ne ba zai tabayi mata zip ta baya ba, a tsakiyar skirt din, ta gefe yakeyi mata, kuma duk yanda zata motsa, bai taba budewa ba, matsaloli biyu ne, karamar shine tsayin yankan zip din ya sauka sosai, babbar matsalar karamin wandone kawai a jikinta, ita ba underskirt take sakawa ba, yawancin gajerun wanduna ne masu kama jiki, to data saka sai taji skirt din atamfar ya wani irin matseta har bata numfashin kirki, saboda anyi shafi ta ciki, yadin da akayi shafin irin mai kaurin nan ne, dole ta cire gajeran wandon tana barin pant kawai, gyale ne a jikinta, gyalen da tasan babu wani abu da zai rufe mata.
Tsabar yanda ta kidime ma ta manta da dabkwalin da yake kanta, gabaki daya ta rasa abinda zatayi, jikinta har rawa yakeyi, ga wannan tarin mazan da ta kula wasu hankulansu na kanta, ga mutanen da suketa zirga-zirga, dole ma idon wani yakai kanta, ga shi kanshi wandon na ciki ba wani abu ya rufe mata ba, zuciyar da take bata shawarar ta zunduma ihu take shirin biyewa kafin taji mutum a bayanta, ta kuma ji kamar wani abune ya rufa mata, jin kamar hannuwanshi yake shirin zagayowa ta kugunta yasa tayi saurin rike koma menene yake kokarin daura mata, sai taga hannuwan rigane, riga mai laushi, cikin rawar jiki ta zagayasu tana daurawa kafin ta juya kanta ta dan dagashi tana saka idanuwanta cikin nashi da ya kankance yanayi mata wani kallo.
Bata sanshi ba, haka kawai taji ta fahimci wannan kallon, ta kuma gane ranshi a bace yake, kallo ne yakeyi mata kamar yana shirin kifa mata mari, kaifin kallon nashi ne yasa ta sauke nata idanuwan babu shiri, ji tayi tana son ta fadi wani abu da zata kare kanta, dan a kasan wannan bacin ran, taga kamar harda tuhuma
"Um, daman, daman..."
Ta daburce tana rasa abinda take so ta fada, kallon dai yakeyi mata, dan karamin tsaki yaja, taji karar tsakin
"Ai skirt din tsoronki yakeyi da zaki saka kanki a cikinshi yaki budewa ko? Saboda baki da hankali wannan skirt din zaki saka ki fito dashi..."
Ta kalle shi daga farko, ko tace idanuwanshi ta gani, yanzun data kara dago kanta shi din ta gani, gabaki dayanshi. Dogone, kusan zaifi Khamis tsayi ma, amman Khamis farine tas, wannan kuma kai tsaye ba zaka kirashi da fari ba, akwai wani abu a fuskarshi da kai tsaye ba zatace menene ba, amman abinne ta gani tasan ko ta rantse ba zatayi kaffara ba, dan uwan Khamis ne. Babu wani abu kai tsaye daya bambanta shi da mazan da zaka hadu dasu a titi yau da kullum, muryarshi dai tana da wani irin zurfi da muryoyin maza da yawa suka rasa. Sai da ta sake kallonshi a karo na uku, ta dan ware idanuwanta, rigar jikinshi mai karamin hannu ce kuma ta dan kamashi, da alama ta saman mai dogon hannun itace ya cire ya daura mata.
Wuyanshi take kallo, wasu zanuka ne layi-layi da bata ga farkonsu ba, karshen take nema, inda zata samu ya juya ma taga ko har ta baya akwai zata so, gasu nan sirara da sukayi wata irin sarkakiya, data daga idanuwanta zuwa fuskarshi sai taga akwai
"Ya ma akayi bata kula da farko ba?"
Tun daga cikin kanshi inda gashi ya boye farkon wannan layin, ta bangaren damarshi, layukan sun tahone har kamar sun biyo ta cikin idonshi guda daya, sukayi wata alama a gefen kuncinshi sai yayi mata kama da walkiya, tunda take a rayuwarta bata taba ganin wani abu irin wannan ba, shi yana da duhu, layukan kuma sunyi wani irin haske sosai, hasken da idan da kalar fata zata auna shi zatace kwatankwacin hasken zabiya.
"Tattoo ne?"
Tambayar ta subuce mata, ganin yanayin dake idanuwanshi ya sauya lokacin daya yasa ta dan daga hannunta tana dan tattaba fuskarta, tana masa alama da abinda yake tashi fuskar take magana akai
Yaji tambayar da tayi,
Ya gane abinda take nufi...
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: Abinda bai gane ba, dalilin da yasa ranshi bai baci ba, a karo na farko a tsayin shekarun da zai tuna da wani yake kare masa kallo haka, kuma harya hada masa da tambaya irin wannan amman bai harzuka ba. Ko dai yanayin yanda tayi tambayar da dukkan gaskiyarta ne? Sai ya girgiza kai yana kara jan wani karamin tsakin kawai ya raba ya wuceta. Sai kiran wayar Khamis yakeyi baisan inda ya ajiyeta ba da bai daga ba, a gajiye yake saboda rashin wadataccen bacci, harya watsa ruwa zai kwanta ya kirashi yace zai karbo masa sako a hotoro.
Ya aiko masa lambar wanda zai karbi sakon a wajenshi, sai da ya hau mashin yaje da nufin ya karba mai mashin din ya dawo dashi, sai yaga lemuka ne da ruwa sama da katan goma sha biyar kowannensu, gashi babu wasu kudi a jikinshi, bai fita da atm ba balle ya cire, layin ma da zaiyi transfer ba'a kan wayar yakeyi ba, kuma ya dinga jerawa Khamis kira har hudu bai daga ba, ya taho ya kusa gida Mummy ta dinga kiranshi, yasan ba wani abin arzikin bane, shisa yaki dagawa, ganin ba daina kiran zatayi ba yasa ya dauka, sai kuwa ta sauke masa wani zagi cikin kunne tana dorawa da
"Lallai Faruku, ni zan dinga kiranka kaqi daga wayar saboda iskanci, zuwa zakayi kayiwa Taj magana ya kwashemun yan kan uban tantiran daya kwaso ya kawomun kofar gida kafin in kira 'yan sanda su tattare mun su wallahi..."
Baice komai ba ya kashe wayar kawai, baisan meye matsalar Taj da janyowa Mama Babba magana ba, ya shigo gidan da wannan bacin ran ya hango ZamZam a tsaye. Karamin wandonta ya fara gani, ja, da abinda ya rufe mata ba wani mai yawa bane, sai kuma cinyoyinta, bakaken cinyoyinta da har daukar ido fatar da ta lullubesu takeyi, yaji wani irin abu ya dirar masa, ya waiga gefe da gefe yana fatan shi kadai yaga abinda yagani, yana addu'ar shi kadai ya ganta, tun kafin ya karasa wajen ya cire rigar jikinshi, ya kuma kara saurin tafiyarshi, batare da tunanin komai ba yayi niyyar zagaya hannuwanshi ya suturta mata jikinta ta hanyar daura mata rigar a kugunta. Data juyo sai kawai yaji yana son ya kifa mata mari.
Anya tana da hankali? Tasan yanda take? Ko kuma yace taga yanda take? Me yasa zatayi tunanin saka wadannan cinyoyin...
Sai ya girgiza kanshi yana furta
"Astagfirullah..."
Ya za'ayi ta saka jikinta a cikin wannan skirt din kuma tayi tunanin zai dauketa. Da ya tambayeta maimakon ta amsa saita tsaya tanayi masa wata tambayar ta daban, kamar babu abinda ya faru, kamar zip dinta bai bude ba, sai kawai bacin ran daya dan barshi na wasu mintina ya sake dawo masa, musamman ma da a wannan lokacin, daya daga cikin makidan nan ya kafa bakinshi a jikin wani kaho yana busawa, wani daban kuma yana tsakiyar taron yana ma kanshi kirari
"Gudu cinikin kare, daga ba kare ba sai dai doki...mai kidan maza kidan artabu...kowa yasan duka baya sa mu canza halinmu, dauri bayasa mu canza halinmu, ki gudu sa gudu amanar Taju..."
Sai aka kara jan wata irin busa wajen ya dauki sowa, sai ya hango Taj ya shigo tsakiyar taron nan, bakin wando ne a jikinshi sai rigar saki bula, ga wata sarka ta farin murjani a wuyanshi, yana shiga filin kuwa sautin kidan ya sauya zuwa wasu ganguna da suka saka Faruk tsayawa kallon ikon Allaah, ba zaiyi karya ba, kidan yayi masa dadi a kunnuwanshi, Taj yayi kasa-kasa ya dago sama, sai wani ya fito ya shigo filin yayi masa jinjina irin ta manyan 'yan daba
"A lafiya Taju jinin yarabawa, baka gudu kabar abokin gaba, daka gudu gara ka fadi..."
Aka kwaso wata ashariya mai idgami data sa Faruk ratsawa ya shiga tsakiyar taron ya kama hannun Taj daya juyo fuskarshi dauke da murmushin da baka rabata dashi, ko shi zai bayar da shaida akan Taj baya shan komai a yanzun, amman wannan alamar ta ya taba sha a baya na bayyane akan labbanshi
"Dan Mamaa"
Ya fada cikin maganarshi da ta zame masa jiki
"Taj ya mukayi da kai?"
Dariya yayi
"Allaah Ya kara maka lafiya Dan Mama, nifa Kham yayi mun clearance shisa kaganmu nan muna dan rakashewa, matar can ce ta kiraka ko? Nan fa ta fito tasha wasu korayen kaya yanda kasan bishiyar lemon tsami zatayi mana eh yane, amman banyi magana ba saboda bana so ran Babba ya baci"
[11/1, 10:25?AM] +234 803 948 4704: LubnaSufyan ?
#WomenOfWords
#09035723778 (Whatsapp number)
Littafin nan na kudine da za'a iya samunshi a manhajar Arewapen a yanzun, bayan mun kammala shafuka biyar na dandano. Zai kuma zo a manhajar telegram bayan wani lokaci In Shaa Allaah.
To Aisha Abdu Gusau, with Love.
FACALA
No comments