Recent Updates

MARAICIN YA MACE Page 9&10

 


Washegarin ranar, gidan Malam Bala ya wayi gari cikin hayaniya kamar yadda aka saba. Inna Salame tana zaune a tsakar gida tana gyaran wasu kayan miya, yayin da Bintu ke can gefe tana share ƙofar gidan...kamar yanda ta saba ,tamkar ba mugun duka tasha a wurin Inna salame ba , kowa har ko kin sa yake yi a cikin gidan ,Duk da cewa shekarunta goma sha biyar kacal a rayuwa amma Inna ta riga ta ɗora mata nauyin da ya fi ƙarfin shekarunta. Ba ta da lokacin wasa irin na sauran 'yan matan da suke sa'anninta, domin tun da sassafe sai aiki , kamin hantsi tallah idan ta gama sayar dana safe , ta dawo ,ta ɗauki na Rana , idan ta dawo ta ɗauki na dare , a haka take babu boko babu Arabi ” .,sannan idan ta dawo kuma sai ta ci gaba da sauran ayyukan gida. A wannan lokacin ne Sahura, ƙawar Inna Salame, ta shigo gidan tana sallama. Sahura mace ce mai son gulma da shiga al'amuran mutane, amma tana da wata irin ƙwarewa wajen neman hanyoyin samun kuɗi. “Salame! Ina kika ɓuya ne? Na zo sau biyu ban same ki ba.” Salame ta ɗago kai tana murmushi. “Sahura, ai kin san gidan nan kamar naki ne. Ki shigo mana.” Sahura ta zauna a bisa Tabarmar da Inna ke zaune , yayin da Sauran matan Gidan ke gaishe ta . Nan suka fara gaisawa kafin ta kalli Bintu da ke sharar tsakar gidan “Wannan yarinyar har yanzu tana nan , ai Ni ɗauka yanzu warhaka an Aurar da ita. ? Ai na yi tunanin kin riga kin samu mata gidan aure.” tayi maganar cike da gulma da son jin tsegumi.... Salame ne ta yi wani irin tsaki. “Kai Sahura, kada ki tuna min da ɓacin Rai. Shekara goma sha biyar fa take yanzu, amma har yau babu wanda ya zo ya ce yana son ta. Ni kam na gaji da zama da ita wallahi , ko da yake tayiwuwa idan ta fita talle maza na shigar da ita Lungu su ƙwaƙule Gindin , Tun da jiya da ta Ɗau tallah da Dare wallahi sai Tsakar dare yarinyar nan ta shigo , kina Ganin haka Simimi kasau sheɗaniya ce ....  Buɗe baki Sahura ta yi tana Wani irin dariya kaɗan. “To me ya hana ki aurar da ita? Ko da mai sayar da ruwan amalanke ne, ɗan garuwa mana a'a , muddin zai ɗauke ta daga gidan nan, ai kin huta.” kallon ta Salame ta yi tana dariya, tana mai cewa, “Wallahi kuwa! Ni dai duk wanda zai zo ya ce yana so, zan saurare shi Wallhi ko mai yasar ƙwata ne , don na aura masu ma cucesu don bani da tabbacin Budurcin ta ba'a cinye a lungu da Saƙo Ba .”. Ai gara ta tafi da talaka ta rage min nauyi.” Bintu tana jin maganganunsu ne daga inda take, amma ta yi kamar ba ta ji ba. Zuciyarta ta yi nauyi,  ta san cewa ba don ana son farin cikinta suke wannan maganar ba, sai dai don kawai su rabu da ita...su kuma ƙuntata ma Rayuwar ta .”

Sahura ta sake kallon Salame, sannan ta ɗan matsa kusa da ita. “Amma akwai wata shawara da nake so in ba ki. Me zai hana ki fara neman mata gidan aiki? Akwai gidajen masu kuɗi da yawa a wannan gari na mu. Ana ɗaukar yara mata su yi aikin gida, a ba su abinci da wurin kwana, da albashi duk wata..... Salame ne ta ɗago kai da sauri. “Aikin gida?” gidan Aikatau kenan.  Sahura ta gyada kai. “Eh mana! Na san wani gida mai girman gaske, gidan Alhaji Makama , babban soja ne da yana cikin mutane uku da suka taɓa riƙe muƙamin marshal a soja ... Allah yayi masa Arziƙi ga ƴaƴan sa a yanzu har aƙwai ƴan siyasa .....manya ne fa a ƙasar nan sosai .Mutane ne masu arziki sosai nake faɗa Miki...... kuma suna da ma'aikata a gidansu. Wataƙila za su buƙaci yarinya mai taimakawa wajen ayyukan gida.” ko wanke wanke ne ai zasu iya ɗaukar ta ko share share.  ..Salame ta yi shiru tana nazarin maganar. “Amma kin san halin Bintu, ba ta da ƙarfi sosai , yanda kasan Goji haka take , gata yar gidan talaka amma sai son jiki , Ni fa bai dame ni ba ,indai Albashin da yawa , don haka ko banɗaki zata rinƙa wanke masu Ni bai dame Ni ba Sahura .” Sahura ne ta yi dariya. “Ai ba a ce za ta ɗauki dutse ta ɗora a kanta ba. Za ta yi ayyukan da aka ba ta ne . Ke kuma za ki samu sauƙin rayuwa.” Salame ta yi murmushi a karon farko. “Sahura, wannan shawarar taki ta yi min daɗi. Gaskiya kin kawo min mafita.” Sahura ta ƙara da cewa, “Zan iya taimaka miki wajen gano hanyar da za a kai ta. Saboda naji wata ƙawata tana cewa ” Suna buƙatar yarinya wacce zata yi masu ko aikin Kula da Wani ɓangare ne..? Ni dai na manta . Salame ta yi saurin amsawa, “Ai muddin za su karɓe ta, ni ban damu da komai ba.” Sahura ta kalleta, ta ɗan yi shiru, domin ta fahimci cewa Salame ba ta tunanin makomar yarinyar sosai. Miƙewa tayi tana gyara wata bangajejen jakar ta ,irin ta dillalai kana tace ” Bara na wuce kin san gidan yawa da tsegumi kamin ace Na zo na hure miki kunne akai Marainiya Aikatau .....” 


Miƙewa Inna tayi tana taka mata zuwa Zauren Gidan ,tare da cewa ” Ai don Allah ki mun ƙoƙari daga yau zuwa Gobe a samar mata da Wannan aikin , masu gulma kuma sun daɗe basu yi ba ,Yauwa ” . Uban ta kullum nema yake Daƙyar . Kullum idan mun daura tukunya tho tuwon Da wace ko ta masara . Don haka Nagode sosai Sahura . Ina sauraren ki zuwa Goben ” . Da haka suka yi sallama ,kamin inna ta koma tana zuba Gyaɗa a ƙwanƙwan tare da Ɗaura ma Bintu tallar tana zuba mata kashedi kada ta dawo bata siyar ba. 



*
A Washegari da safe, Sahura ta zo gidan da wata sabuwar maganar. Inda take kawo masu labarin cewa gidan Alhaji Makama tabbas fa da gaske suna neman ma'aikata, musamman masu taimakawa wajen kula da gida. Salame ta yi farin ciki sosai da jin hakan, a kuma nan take ta kira Bintu daga ɗaki. “Bintu! Zo nan.” Bintu ta fito cikin sauri jikin ta na rawa cike da ladabi ta amsa. “Na'am Inna.” Salame ta kalleta daga sama har ƙasa. “Kin san cewa zaman banza ba zai taimake ki ba. Na samu miki inda za ki je ki yi aiki.” Bintu ta ɗago kai cikin mamaki. “Aiki kuma Inna?” “Eh mana! A gidan masu kuɗi. Za ki yi aikin gida, ki samu abinci da wurin zama da albashi duk wata wanda hakan kamar taimakon uban ki ne .” Bintu ta yi shiru. A zahiri tana jin tsoron barin gidan da ba ta sani ba, amma a wani ɓangaren kuma tana ganin kamar wata dama ce ta samun ɗan sauƙi daga wahalar da take ciki. “Inna, ni zan je?” Ta tambaya cikin sanyin murya. “ ke za ki je mana! Ko kina son ki zauna kina cin abincina har abada ne?” Bintu ta sunkuyar da kai. “To Inna shikenan.” nan Salame ta juya wajen Sahura. “Yaushe za mu je?” Sahura ta ce, “Idan kin shirya, zan iya kai ki wurin mutanen da za su haɗa mu da masu gidan.” Salame ta yi murmushi. “To, shikenan. Amma ki tabbatar an karɓe ta ,na baki wuƙa da nama sahura ba sai naje ba kema zaki iya kaita da hannu. Ki. Ni dai kawai na gaji da wannan yarinyar a cikin gidan nan wallahi . 

Ai kar kiji komai Salame , yanzu zaki huta kudade kuwa ance gidan akwai alheri suna da kyautatawa ma'aikatan su wallahi . Ke tashi ki bamu wuri , Inna Sallame ta furta tana dalla ma Bintu harara ,inda cikin sauri ta miƙe tana barin Wurin. ”


*
A gidan Alhaji Makama kuwa, Hajiya Dr. Saleema tana zaune a falonta tare da wata mata mai kula da harkokin ma'aikata. Ta kalli takardun da ke gabanta, sannan ta ce, “I need someone responsible to assist with the household duties. Amma ina son a tabbatar da cewa duk wanda za a kawo yana da cikakken bayani da kuma wanda za a iya tuntuba daga danginsa.” Matar ta gyada kai. “Insha Allah Hajiya, zan tabbatar da hakan.” Hajiya Saleema ta ci gaba da duba takardunta ....a hankali ta furta ” Suhail yana Falon sa , kun san shi ma'abocin shan cofee ne , a kai masa yanzu . Tayiwuwa yau ba zai fita bane.  Ohk Hajiya , ma'aikaciyar ta furta , kamin tace ” Yauwa Hajiya nace , Ya kamata a samar ma Suhail da Personal maid wacce iya cofee zata rinƙa kai masa , Saboda kin san shi , shi har cikin dare shan cofee yake.  Shiru Hajiya tayi kamin tace ” Alright zan yi tunani akan hakan .



Suhail ne yana zaune a ɗakin karatu yana duba wasu takardun kamfaninsu....don shi mutum ne mai harkoki da yawa , kasantuwar sa Doctor bai hanasa zama Da kasuwa ba....nan ƙarar knocking ya katse sa inda nan take ya Ɗago yana furta. “Come in.”



 Wani ma'aikaci ne ya shigo yana sanar da shi cewa an samu labarin yarinyar da ya nemi a bincika masa. Cikin sauri Suhail ya ajiye takardar hannunsa. “An same ta?” Ma'aikacin ya amsa masa da , “Ba mu tabbatar da ita gaba ɗaya ba, amma mun samu wani bayani game da inda take.” Suhail ya ɗan yi shiru, sannan ya ce, “Ku tabbatar da gaskiyar bayanin. Kuma ina son a kula da duk wani abu da ya shafe ta. Ba na son a zalunce ta wurin kawo mun ita da ƙarfi ,sannan kada ku bari Mummy ta samu wannan labarin.”ohk Sir.  Nan  Ya koma duba takardunsa, amma zuciyarsa ba ta nan. Ya tuna da idanun yarinyar da yadda ta kasance cikin tsoro a daren da suka haɗu. Bai san dalilin da ya sa yake jin kamar akwai wani abu a cikin labarinta da bai gama ganowa ba......Shidai tun da ya ganta ya kasa mantawa da ita , Yanda take masa magiya da ihu tana furta ”aljani ya tuno ,nan ta saki wani Murmushi tare da Duban 🍌 Hajiya babban sa Wanda yasan itace ta firgita yarinyar .” .

No comments