MARAICIN YA MACE Page 7&8
Da misalin ƙarfe goma sha ɗaya da rabi na dare, Bintu ta ƙaraso ƙofar gidan Malam Bala cikin tsananin gajiya. Ƙafafunta sun yi nauyi, idanunta sun kumbura saboda kuka, zuciyarta kuwa cike take da tsoro. Ta tsaya a bakin ƙofar tana kallon cikin gidan, kamar wadda ba ta san ko ta shiga ko ta juya ba. A ƙarshe ta tattara ƙarfin halinta ta tura ƙofar a hankali. Kafin ta kai ga shiga, sai muryar Inna Salame ta daki kunnenta. “Ke! Ashe har yanzu kina da fuskar dawowa gida? Ina kika je tun ɗazu har dare ya yi haka? Kin ɗauka ni wawiya ce da za ki yi ta yawo kina tunanin ba zan tambaye ki ba? , ko ban san gantalewar da kike yi da maza ba” Bintu ta sunkuyar da kai, hawaye suka fara zuba mata. “Inna, wallahi…” “Rufe min baki! Ba na son jin wani uzuri daga gare ki. Na ba ki amana, na ce ki je ki sayar da gyada ki dawo da kuɗi, amma sai ki ɓace kamar wadda ta tafi wata duniya!” Salame ta miƙe tsaye cikin fushi, ta cafke Bintu ta fara yi mata wani irin dukan tsiya cike da rashin tausayawa .Bintu ce ta durƙusa tana kuka tana roƙon ta da ta saurare ta, amma Salame ta ƙi ba ta dama. Mutanen gidan suna kallonsu ne kawai; wasu sun kawar da kai, wasu kuma suka yi shiru saboda tsoron shiga lamarin Salame. Baraka kuwa tana tsaye a gefe, zuciyarta na zafi saboda halin da Bintu take ciki, amma tsoron abin da Salame za ta yi mata ya hana ta motsawa. “Inna don Allah ki saurare ni, ban yi laifin da kike tunani ba…” Bintu ta faɗa cikin kuka. “To mene ne kika yi? Ina kuɗin? Ina gyadar? Ina kika kwana?” don kin ƙarar da rabin daren ki a titi Salame ta katse ta. Bintu ta kasa amsawa, domin ba ta san ta ina za ta fara bayyana abin da ya faru ba. Ta tuna yadda aka yaudare ta, yadda ta tsere daga gidan ba tare da ta san inda za ta dosa ba, da kuma yadda ta ƙi karɓar kuɗin da aka ba ta. Ta ji kamar duk duniya ta juya mata baya. Bayan Salame ta gama fushinta, ta nuna mata wani ɗaki da ko awakai bana jin za'a iya barin su su ƙwana ,amma anan ne Wurin barcin Bintu....yi ta kanki amma wallahi zuwa gobe duk inda Farantin gyaɗan da kuɗi na suke ki nemo mun su ..... “Je ki can ki kwanta. Gobe kuma sai kin bayyana min inda kika je da abin da ya faru. Idan kuma kika sake ɓoye min gaskiya, za ki ga abin da ba ki taɓa gani ba!” Bintu ta miƙe a hankali, jikinta a sanyaye, ta wuce gefe tana share hawaye. Baraka ta bi ta da kallo, amma ba ta iya cewa komai ba ,da ɗingishi ta shige Ɗakin ta inda ya kasance tabarma ce kaɗai sai wata mitsikakken zangon ta na rufa ” .
*
A can kuwa, a gidan manyan mutanen masu hannu da shuni,wato familyn Makama, Hajiya Dr. Saleema tana zaune a babban falonta tana duba wasu takardu na asibitocinta. Ita mace ce mai ilimi sosai, wadda ta yi karatun likitanci har ta kai matsayin da take da asibitoci a jihohi daban-daban na ƙasar nan. Ba wai ilimi kaɗai take da shi ba, tana da basira da iya magana, kuma ba ta son a raina mata hankali, aƙwaita da Zafi. A lokacin da Suhail ya dawo gida, ya tarar da ita har yanzu tana zaune a tsakiyar ƙayataccen falon ta. “barka da Dare, Mum.” Ya faɗa yana ajiye makullin motarsa. Hajiya Saleema ta ɗago kai ta kalle shi. “barka dai Suhail. Ta furta tana gyara zaman medicated eye glass ɗin ta,kamin cikin harshen nasara ta fara cewa”. You said you were on your way, but it took you quite a while. Where exactly were you?”
Jin maganar ta yasa Suhail ya ɗan yi murmushi kaɗan ,yana ƙaƙaro maganar da zai faɗa mata “Sorry Mum, something came up. I had to sort it out before coming home.” shiyasa na Ɗan jima ban dawo ba . Hmmm Nan Ta ajiye takardun hannunta, ta gyara zamanta tana mai cewa”. “Suhail, I hope you understand that I don't like excuse, kasan tun ba yauba by 10:pm Yana Yi maka ne a cikin gida , Saboda Kai ba mutum ba ne mai son Escort ko securities da zasu baka tsaro . Sannan kasan Waye kai kuma waye Mahaifin ka...? .” “I understand, Mum.”
“Good. Kuma ka tuna da dokar gidan nan. A nan ba mu barin yaranmu maza su yi aure sai sun kai shekara talatin da biyar. Bashir da Yazid sun bi wannan ƙa'ida, kuma kowannensu yana da iyalinsa yanzu. Kai kuma har yanzu kana ƙasa da shekara talatin. Kada ka bari jin daɗin duniya ya sa ka manta da tarbiyyar da aka ba ka ,da kuma tsarin mu , kada don kana da Kuɗi ka shagala da Tsarukan cikin gidan mahaifin ka , ta furta tana mai kafe sa da ido , don ta fara lura yana ji da Giyar kuɗi , kuma ko mene Ɗan ta zai yi a tafin hannun ta take kallon sa ....duk da kasancewar Suhail na da matuƙar wayo duk abubuwan sa da yake yi da matan bariki baya yarda Wani nasa ya sani. Suhail ya ɗan yi shiru, sannan ya amsa, “I know, Mum. Ban manta ba.” Hajiya Saleema ta sake kallonsa da kyau. “Ina fata. Domin dukiya ba ita ce komai ba, Suhail. Allah Ya ba ka arziki, amma hakan ba yana nufin ka yi rayuwa yadda kake so ba tare da tunanin sakamakon ayyukanka ba.” Suhail bai ƙara cewa komai ba. Ya san mahaifiyarsa ba mace ce da za a iya yaudararta da magana kaɗai ba. Nan Ya yi mata sallama ya nufi ɗakinsa, amma tunaninsa ya dawo kan yarinyar da ta gudu daga gidansa a wannan daren. Ya girgiza kai kamar yana son korar tunanin, sannan ya zauna a gefen wani irin ƙayataccen gadonsa. “What a terrible night!” ya faɗa a hankali yana Lumshe dulu dulun idanun sa , tare da jingina bayan sa da pillow .
A gidan Malam Bala kuwa, Bintu ta kasa yin barci. Tana kwance a lungu tana tunanin yadda rayuwarta ta kasance. Ta rasa wanda zai saurare ta, wanda zai kare ta, ko kuma wanda zai tambaye ta dalilin da ya sa ta dawo cikin wannan halin. Ta rufe fuskarta da hannaye tana kuka a hankali, har barci ya ɗauke ta saboda gajiya. Baraka kuwa ta fito daga ɗakinta a hankali, ba tare da ta bari Inna ta ganta ba , tana shigewa dakin da Bintu ke a ƙwance ,nan ta tsaya kusa da inda Bintu take kwance. Ta kalle ta na ɗan lokaci, sannan ta yi ajiyar zuciya. “Allah Ya taimake ki, Bintu,” ta faɗa cikin zuciyarta, kafin ta koma ɗakinta jikin ta a sanyaye ganin halin da yarinyar take ciki,kuma babu mai taimakonta sai Allah,don kowa a gidan tsoron Inna yake ji ciki kuwa har da mijin nata ......!

No comments