Recent Updates

MARAICIN YA MACE Page 11&12

 
A washegari da sassafe, Bintu tana zaune a bakin ƙofar ɗakin Inna tana aikin wahalar data Saba . Duk da na yau da Sauƙi Surfen Wake ne take yi , yayin da zuciyarta ke cike da tunani iri-iri. Tun daren jiya take tunanin maganar Inna Salame na cewa za ta kaita gidan aikatau. Ba wai tana tsoron yin aiki ba ne, domin tun tana ƙarama ta saba da wahala iri iri , da izaya na Inna. amma abin da ke damunta shi ne rashin sanin irin mutanen da za ta tarar a gidan da za ta je....tun bayan faruwar Abin da ya faru da ita a wancen daren ya zamana tana Tsoron mutane sosai ......A lokacin da take cikin wannan tunanin ne Malam Bala ya fito daga ɗaki, yana riƙe da carbi a hannunsa.idanun sa ne suka sauka akan bintu yana kallon ta , yana furta  “Ke Bintu!,  da Sauri ta Ɗago idanun ta tana furta Baba , Ina kwana?” .


Ɗan kallon ta yayi kamin ya tambaye ta ”me ya sa kika yi shiru ,Tunanin mene kkyi haka?” Bintu ta ɗago kai cikin Sanyi kamin cikin zaƙin Muryar ta tace “Babu komai Baba.” ɗan gyarar murya yayi kamin yace”, “Na ji Inna tana cewa za ki tafi gidan aiki yau. Gaskiya ne?” Bintu ta ɗan yi shiru kafin ta amsa, “Eh Baba, Inna ta ce an samo min aiki a gidan wasu masu kuɗi.” Malam Bala ya sauke ajiyar zuciya. “To Allah Ya sa alheri ne. Amma ki sani, duk inda kika je, kar ki manta da kula da kanki da kuma ibadar ki ... Ki kasance mai gaskiya da ladabi,.” Jin waɗannan kalaman ya sa idanun Bintu suka cika da ƙwalla. Ta daɗe ba ta ji wani ya yi mata magana cikin tausayi irin wannan ba. A hankali ta furta  “Nagode Baba. Yauwa bintu ,ni yanzu zan wuce kasuwa sai na dawo . Tho A dawo Lapiya baba Allah ya tsare.  Ta furta yana mai ficewa daga gidan , a kuma dai dai lokacinne Inna ta buɗo labule tana fitowa tare da bin ta da kallon banza ,kamin tace ” Munafukar banza , ai dama kinyi gadon halin uwar ki na munafurci , a lokacin da take raye ba ƙaramin wahala nasha da kissa da kisisina ba ,ayi ta ma miji shine kyama zaki Ɗauka? , ai dama barewa ba tayi gudu Ɗan ta yayi rarrafe ba ,munafuka Ni Uban ki zaki ci Wallhi kin saanni sarai . Tuni idanun Bintu suka ciko da Ƙwallah , a hankali tayi ƙasa da kanta tana cewa ” Kuyi haƙuri Inna . Nan taja tsaki tana wuce ta ba tare da ta kuma bi takan ta ba .







Bayan ɗan lokaci, Sahura ta iso tare da wata mata da ta ce za ta taimaka wajen kai Bintu gidan Alhaji Makama. Wani irin farin ciki Inna keyi ,don tasan a yanzu kuɗaɗe zasu ƙara shigo mata tun da dama ita irin matan nan masu sana'a goma da Ashirin .Anan suka Gaisa da mutanen Gida kamin, suka ɗauki jakar Bintu, wanda ya kasance kayan ciki duk babu na Azo a gani ,duk tsummoki ne ,shima jakar ya tsufa tukufff .....sannan suka nufi hanyar gidan Dr Salima. A lokacin da suke tafiya, Bintu tana kallon titi ta cikin motar da suka shiga, tana tunanin yadda rayuwa za ta kasance a sabon wurin da za ta tsinci kanta. Ba ta san cewa tafiyar da take yi za ta haɗa ta da wani sabon babi na rayuwarta ba......! Muje zuwa dai kar ku manta wanda basuyi payment ba ,wannan shine last free page , daga wannan ba zaku sake samun update ba sai iya waɗan da suka biya kuɗin su zamu saka su a GRP .




A lokacin Da suka isa gidan Alhaji Makama, Bintu ta kasa ɓoye mamakinta. Gidane girma iya girma sosai ,ga ƙayatuwa kai dagani kasan gidan masu faɗa a jinne a wannan ƙasar, akwai manyan motoci a harabar gidan, lambuna masu kyau da kuma ma'aikata da suke ta kai-komo. Ga sojoji dake kai kawo .Ta sauka daga motar tana riƙe da jakarta da hannu biyu. Sahura ta kalleta ta ce, “Bintu, nan ne gidan fa. . Ki kasance mai ladabi, ki riƙa bin umarni, kuma kada ki yi abin da ba a ce ki yi ba.” Bintu ta gyada kai a sanyaye kamin tace “To.” Anan suka fara shiga cikin gidan.



A falon gidan kuwa, Hajiya Dr. Saleema tana duba wasu takardu lokacin da aka sanar da ita cewa an kawo yarinyar da za ta fara aikin. Ta ce a shigo da ita kai tsaye ,don tana buƙatar sabuwar ƴar aiki.... Bayan ƴan mintuna, Bintu ta shigo cikin nutsuwa, kanta a sunkuye, gaba ɗaya wurin yayi mata ƙwarjini inda bata taɓa tamanin ƙafarta zai kawo ta ba .hannunta riƙe da ƙaramin jakarta. Hajiya Saleema ta ɗago kai tana kallonta. Da farko ta yi mamakin ƙanƙantar yarinyar, wannan yasa ta cewa ” Kece mai Aikin .? Hmmm ta furta tana Numfasawa tare da tsayar da idanun ta bisa kan Bintu ,wacce cikin sauri jiki na rawa tace ” Barka da safiya Hajiya . Hmmm juyawa Hajiya Saleema tayi kamin ta  tambayi Sahura, “shekarunta nawa ne?” Sahura ta yi saurin amsawa, “ba zata wuce 15 ba Ranki ya daɗe , Hajiya.” Hajiya Saleema ta ɗan zaro ido. “Fifteen? She's still very young!” (Shekarunta goma sha biyar? Ai har yanzu yarinya ce ƙarama, Ta kalli Bintu da kyau, sannan ta tambaye ta cikin tausasawa, “yq sunan ki?” Bintu ta amsa a hankali, “Sunana Bintu, Hajiya.”


 Hajiya Saleema ta gyada kai. “Okay, Bintu Fatima kenan suna mai daɗi , Kin yi karatu ne?” Bintu ta girgiza kai. “A'a Hajiya, ban yi ba.” Hajiya Saleema ta ɗan yi shiru, sannan ta kalli Sahura....a hankali ta juya ga Babban mai aikin ta Wato Ruth tana faɗin “Honestly, I wasn't expecting someone this young. I don't think she should be given heavy household duties.” (Gaskiya ban yi tsammanin za a kawo min yarinya ƙanƙanuwa haka ba. Ba na ganin ya dace a ɗora mata ayyuka masu nauyi.) Sai ta juya ga Bintu tana cewa, “Daga yau, aikin da za ki riƙa yi shi ne sharewa da goge-gogen ƙaramin ɓangaren gidan da ke kusa da ɗakin Suhail. Za ki riƙa kula da tsaftarsa ne kawai, kuma ba za ki shiga ɗakin kowa ba sai da izinina. Idan wani abu ya dame ki, ki sanar da ni. Kin ji ko kina buƙatr wani abu?” Bintu ta amsa, “thom Hajiya ngd.” Hajiya Saleema ta ƙara da cewa, “Kada ki ji tsoron tambaya idan ba ki fahimci wani abu ba. Anan ta cigaba da mata bayanin aikin da zata yi wanda bayan ta gamw ne Hajiya Saleema ta umarci wata ma'aikaciyarta mai suna Maryam da ta nuna wa Bintu inda za ta ajiye kayanta . 

Bayan Maryam ta nuna mata inda za ta ajiye kayanta, a wani ɓangare ne inda ta shiga da ita Ɗaki ba babba madaidaici da Gado da katifa da komai ,sai a sannan ta fara bayyana mata yadda za ta riƙa gudanar da aikin. Sannan ta nufo da ita inda Zata rinka gyarawa kullum .....Amma kafin su gama, sai suka a ji muryar sa ya katse su cikin Dakakkiyar Muryar nan nasa daga bayan su yana cewa, “Maryam!” 


Maryam ne ta juya da sauri. “Yes, Sir.” Suhail ne ya fito daga cikin wani ɓangaren gidan sanye da farar shadda mai kyau, agogon hannunsa na ƙyalli, yana riƙe da wayarsa. Ya kalli Maryam sannan ya ce, “Who is this?” ya furta yana kafe ta da idanun sa don ba zai manta da Wannan fuskar ba , wacce ta gagara basa Haɗin kai a wancen daren , duk da jarabben sha'awar ta da yake yi a kwana kin nan domin yasa a nemo masa ita ruwa a jallo, sai gashi ya ganta a cikin gidan su matsayin Ma'aikaciyar shara,wanda ko kaɗan bai tsammanin hakan ba cikin sauƙi .....Maryam ne ta amsa, “Sabuwar ma'aikaciya ce, Sir. Sunanta Bintu. Hajiya ce ta ce za ta riƙa kula da wannan ɓangaren.” Suhail ne ya karkata kansa cike da rashin kunya yana kallon Bintu. Ita kuwa sai a sannan ne  ta ɗago kai ta haɗa ido da shi, wanda nan take ta gane shi.... A lokaci guda .

Murmushi yayi yana furta, “You?”nan Bintu ta ji gabanta ya faɗi. Ta tuna da daren da suka haɗu da shi,..........




No comments